Mayakan ISWAP Sun Farmaki Ofishin 'Yan Sanda a Jihar Arewa, Sun Bindige Jami’ai

Mayakan ISWAP Sun Farmaki Ofishin 'Yan Sanda a Jihar Arewa, Sun Bindige Jami’ai

  • Mayakan kungiyar ta'addanci sun farmaki ofishin 'yan sanda a garin Gajiram, karamar hukumar Nganzai ta jihar Borno
  • An rahoto cewa 'yan ta'addan da suka bude wuta sun yi ajalin jami'an 'yan sanda hudu da ke bakin aiki
  • Zuwa yanzu rundunar 'yan sandan jihar bata fitar da wata sanarwa ba a hukumance kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Borno - Wasu mayakan kungiyar ISWAP sun farmaki ofishin 'yan sanda a karamar hukumar Nganzai dake jihar Borno, inda suka kashe akalla jami'an 'yan sanda hudu da kwashe makamai.

An rahoto cewa mayakan kungiyar ta'addancin sun farmakin ofishin 'yan sanda a garin Gajiram, karamar hukumar Nganzai sannan suka budewa jami'an dake bakin aiki wuta.

Kara karanta wannan

Ebonyi: An yi musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindiga, an kashe jami'i daya

Mayakan ta'addanci sun farmaki ofishin 'yan sanda
Mayakan ISWAP Sun Farmaki Ofishin Yan Sanda a Borno, Sun Bindige Jami’ai Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

A cewar majiyoyin tsaro, maharan sun kona wani bangare na ofishin 'yan sandan a lokacin faruwar lamarin a daren ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta 'yan banga ta ce:

“An samu rudani a garinmu a daren jiya. Mayakan na ISWAP sun kai hari ofishin ‘yan sanda dake Gajiram. Sun sha kan ’yan sandan da ke bakin aiki.
"Mun tsinci gawarwaki 'yan sanda hudu wadanda suka rasa rayukansu a safiyar nan, wasu jami'an 'yan sanda basu dawo ba har yanzu da muke magana."

Wata babbar majiya ta tsaro ta ce maharan sun bar wajen kafin sojoji suka iso.

Majiyar ta ce:

"Eh, lokacin da muka samu rahoton, dakarunmu sun taru sannan suka isa wajen, amma abun bakin ciki maharan sun tsere."

Rundunar 'yan sanda bata fitar da wata sanarwa ba kan lamarin har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun kutsa cikin fada sun harbe Sarki, an yi awon gaba da mai dakinsa

Jihar Borno ta fuskanci hare-hare daga 'yan ta'adda a baya-bayan nan.

'Yan ta'adda sun farmaki ofishin 'yan sanda

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani abun fashewa da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka dasa shi ya halaka manoma su bakwai a jihar Borno.

Lamarin dai ya afku ne yayin da ƴan ta'addan suka dasa bam ɗin a kan titin Pulka/Firgi da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar ta Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel