Zaben Cike Gurbi: PDP Ta Bankado Yadda Ake Amfani da Jami’an Tsaro Wajen Sayen Kuri’u a Kaduna

Zaben Cike Gurbi: PDP Ta Bankado Yadda Ake Amfani da Jami’an Tsaro Wajen Sayen Kuri’u a Kaduna

  • Jam'iyyar PDP a jihar Kaduna ta koka kan yadda wakilan jam'iyyu ke sayen kuri'u a rumfunan zaben cike gurbi da ke gudana a jihar
  • Ta bakin wani wakilin jam'iyyar a rumfar zabe mai lamba 009 a Barnawa, Kaduna ta Kudu, ya ce akwai sa hannun jami'an tsaro
  • Ya yi ikirarim cewa jami'an tsaro na kallo ana sayen kuri'u ba tare da sun hana ba, lamarin da ya ke kallo barazana ga dimokuraɗiyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Wani wakilin jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, Yusuf Abubakar, ya zargi wasu jami'an tsaro da sa hannu a sayen kuri'u da ake yi a zaben cike gurbi da ke gudana a jihar.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya fadi abu 1 tak da zai iya fitar da 'yan Najeriya daga kangin da suke ciki

Da ya ke zantawa da Channels TV a ranar Asabar a rumfar zabe ta 009 a Barnawa, Kaduna ta Kudu, Abubakar ya koka kan yadda ake sayen kuri'u a rumfar zaben.

Zaben cike gurbi: "Ana amfani da jami'an tsaro wajen sayen kuri'u a Kaduna
Zaben cike gurbi: "Ana amfani da jami'an tsaro wajen sayen kuri'u a Kaduna - PDP. Hoto: KOLA SULAIMON
Asali: Getty Images

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Idan har ka zagaya, za ka ga yadda mutane ke sayar da kuri'un su. Kuma a bayyane ake yin komai babu wata fargaba."

Jami'an tsaro na da sa hannu a sayen kuri'u - Abubakar

Da aka tambaye shi ko wakilan jam'iyyu na sayen kuri'u gaban jami'an tsaro, Abubakar ya ce:

"Kwarai kuwa hakan na faruwa, hatta su kansu jami'an tsaron suna da hannu a ciki, abin da zan iya cewa kenan kawai."

Sai dai bai yi tsokaci kan ko jami'an hukumar INEC na sane da batun sayen kuri'un ba, inda ya ke zullumin mutane za su zabi wadanda suka sayarwa kuri'unsu kawai ba cancanta ba.

Kara karanta wannan

Jerin kasashen duniya 5 da ya kamata ka ziyarta kafin su kara yawan jama'a

Ya ce:

"Ba zan iya gane cewa jami'an INEC na sane ko ba su san ana siyen kuri'u ba, amma dai mu wakilan jam'iyya da jami'an tsaro mun sani.
"Yanzu ina cike da damuwa kan cewa za a yaudari mutane su zabi wadanda basu cancanta ba saboda an basu kudi kawai."

Dalilin gudanar da zabukan cike gurbi a Najeriya

Hukumar INEC na gudanar da zaben cike gurbi a kananan hukumomi 80 da ke a jihohi 26 na Najeriya, inda mutane sama da miliyan 4.6 za su kada kuri'arsu a zaben.

Ana gudanar da zaben ne domin maye gurbin 'yan majalisun da suka mutu ko suka yi murabus daga mukamansu, da kuma sake zabe a wasu wuraren da kotun zabe ta ba da umurni.

Sanata Nwoko: Kudirin ba 'yan Najeriya damar mallakar bindiga

A wani labarin na daban, wani dan majalisar dattijai, Sanata Ned Nwoko ya gabatar da wani kudirin doka da zai ba 'yan Najeriya damar mallakar bindiga.

Sanata Nwoko ya ce hakan ya zama wajibi la'akari da yadda matsalar tsaro ta kara ta'azzara a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.