A Karshe, An Bayyana Kudin Kujerar Aikin Hajjin 2024, An Fadi Yadda Musulman Kudu da Arewa Zasu Biya
- Bayan sanar da samun ragi a kujerar aikin hajjin bana, hukumar NAHCON ta sanar da farashin kujerun
- Hukumar ta sanar da cewa za a biya naira miliyan 4.9 a matsayin farashin kujerar duk da ragin da aka samu
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar Jin Dadin Alhazai (NAHCON) ta sanar kudin kujerar aikin hajjin bana ta 2024.
Hukumar ta sanar da cewa za a biya naira miliyan 4.9 a matsayin farashin kujerar duk da ragin da aka sanar da samu.
Nawa maniyyatan za su biya?
Hukumar tun farko ta bayyana biyan naira miliyan 4.5 a matsayin ajiya na shekarar inda mafi yawan mahajjata suka gagara biya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan yada labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar.
Sanarwar ta ce Musulman Kudancin Najeriya za su biya naira miliyan 4,899 a matsayin kudin kujerar, cewar Daily Trust.
Yayin da 'yan Arewacin kasar za su biya naira miliyan 4,699 sai kuma mahajjata daga Yola da Maiduguri za su biya naira miliyan 4,679.
Hukumar ta bayyana tashin kudin kujerar da matsalar tashin dala wanda ya ke kawo tarnaki ga tattalin arzikin Najeriya.
Yaushe wa'adin zai kare?
Har ila yau, hukumar ta bukaci maniyyata su tabbatar sun tura kudadensu zuwa ranar 12 ga watan Faburairu.
Hakan zai bai wa hukumar damar tura kudaden nasu kafin wa'adin karshe a ranar 29 ga watan Faburairu.
A shekarar 2023 da ta gabata mahajjatan sun biya naira miliyan uku da kadan a matsayin kudin kujera, cewar TheCable.
Hukumar ta ce kudin kujerar zai iya kai naira miliyan shida idan da ba a tattauna da hukmomin Saudiyya kan ragin kudin kujerar ba.
An rage kudin kujerar aikin hajji
Kun ji cewa Hukumar NAHCON ta sanar da cewa an samu ragi a kudin kujerar aikin hajjin bana ta 2024.
Hukumar ta ce hukumomin Saudiyya sun rage kudaden ne ta bangaren tikiti da wurin zama da sauransu.
Asali: Legit.ng