Asiri Ya Tonu: An Bankado Babban Sanata Mai Daukar Nauyin Ta'addanci a Arewa
- Hukumomin tsaro sun bankaɗo wani babban Sanata a Arewacin Najeriya mai ɗasawa da ƴan ta'adda
- Hukumomin tsaron dai na zargin sanatan ne da ɗaukar nauyin ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewacin Najeriya
- Majiyoyi waɗanda suka halin da ake ciki kan lamarin sun ce sanatan ya sha yin tarurruka cikin dare da ƴan ta'adda a Abuja
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumomin tsaro sun sanya ido a kan wani Sanata mai fada a ji a Arewa bisa zargin cewa yana jagorantar ta’addanci da garkuwa da mutane.
An gano cewa sanatan wanda kuma ke jagorantar wani kwamiti mai muhimmanci a majalisar dattawa, na ɗaya daga cikin masu ɗaukar nauyin ayyukan ayyukan ta'addanci a Arewa, kamar yadda majiya mai tushe ta shaida wa jaridar Vanguard a daren ranar Asabar.
Manyan majiyoyin waɗanda suka zanta da jaridar, sun baya cewa hukumomin gwamnati na sane da ayyukan rashin kishin ƙasa na Sanatan, kuma nan ba da jimawa ba zai fuskanci hukunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya bayyana cewa:
"Muna sane da dangantakar Sanatan da maƙiyan ƙasa, ciki har da yawan lokutan da ya yi taron dare da masu garkuwa da mutane, ƴan bindiga da ƴan ta'adda a Abuja, babban birnin tarayya.
An kuma bayyana cewa, sanatan wanda ake zargin yana da alaƙa da wani malamin addinin Islama, yana amfani da tasirinsa wajen kawo cikas a binciken hukumomin tsaro.
Wane laifuka ake zargin Sanatan da su?
Daga cikin laifuffukan da ake zargin sanatan da su har da sanin waɗanda suka yi garkuwa da wasu ɗalibai mata na jami’ar tarayya da ke Gusau jihar Zamfara da kuma wasu ƴan bautar ƙasa ƴan asalin jihar Akwa Ibom da aka kama a hanyarsu ta zuwa Sokoto.
Ɗaya daga cikin manyan majiyoyin ya ƙara da cewa:
"Tuni hukumomin tsaro da abin ya shafa suka bankaɗo wani Sanata daga Arewa, wanda shi ne babban mai ɗaukar nauyin ayyukan ƴan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci a sassan Arewa.
"Hasali ma yana alaƙa mai kyau da ƴan bindigan, waɗanda suka addabi yankin Arewa ta tsakiya da kuma yankin Arewa maso Yamma.
EFCC Ta Bankaɗo Ƙungiyar Addini Mai Taimakon Ƴan Ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC, ta banƙado wata ƙungiyar addini da ke yi wa ƴan ta'adda safarar kuɗaɗe.
Hukumar ta EFCC na kuma zargin ƙungiyar addinin da ba marasa gaskiya kariya a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng