Majalisar Jihar PDP Ta Bukaci Cafke Shugaban Fulani Kan Wasu Dalilai 2, Ta Bayyana Zarge-zargen
- Serikin Fulanin yankin Iwajowa a jihar Oyo ya shiga matsala bayan Majalisar jihar ta nemi a kamo shi
- Ana zargin Seriki Chumo da hannu a kisan wani manomi da kuma jami'in tsaron Amotekun da ke jihar a watan Oktobar 2023
- Har ila yau, ana zargin Seriki da kasuwancin siyar da bindigu a yankin wanda hakan ya kara saka shakku a zukatan mutanen yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Majalisar jihar Oyo ta bukaci cafke shugaban Fulani kan zargin kisan manomi da jami'in tsaro.
Majalisar ta tura sakon ne ga kwamishinan 'yan sanda a jihar da ya kama Seriki Chumo na karamar hukumar Iwajowa a jihar.
Mene ake zargin shugaban Fulani a Oyo?
Ana zargin Chumo da hadin baki wurin kisan manomi da jami'in tsaron Amotekun a rikicin da aka yi a Iwere-Ile a watan Oktoban 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamitin Majalisar kan harkokin tsaro ya fitar yayin zaman Majalisar.
Rahoton ya ce kama Seriki Chumo ya zama dole bayan samun wasu makamai a gidansa, kamar yadda The Nation ta tattaro.
Kudirin cafke shugaban Fulani ya isa Majalisa
Har ila yau, ana zargin Seriki da kasuwancin siyar da bindigu a yankin wanda hakan ya kara saka shakku a zukatan mutanen yankin.
Mamban Majalisar da ke wakiltar mazabar Iwojowa, Hon. Ogunsola Anthony shi ya gabatar da kudirin a matsayin matsala da ke da muhimmanci wanda ya kamata a bai wa kulawa, cewar Independent Newspaper.
Wannan na zuwa ne yayin da yankin Kudu maso Yammacin Najeriya ke fama da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan da muke ciki.
'Yan bindiga sun hallaka sarakuna 2
Kun ji cewa wasu mahara sun hallaka manyan sarakunan gargajiya guda biyu a jihar Ekiti.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 29 g watan Janairu yayin da suke dawowa daga wata ganawar tsaro a wani yankin.
Maharan sun farmaki sarakunan ne su uku yayin da daya daga cikinsu ya tsira da kyar inda suka hallaka sauran guda biyun.
Asali: Legit.ng