Ebonyi: An Yi Musayar Wuta Tsakanin ’Yan Sanda Da ’Yan Bindiga, an Kashe Jami’i Daya

Ebonyi: An Yi Musayar Wuta Tsakanin ’Yan Sanda Da ’Yan Bindiga, an Kashe Jami’i Daya

  • Rundunar 'yan sanda ta ce wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun farmaki jami'ansu a Jihar Ebonyi
  • A yayin musayar wutar da aka yi ne wani dan sanda ya rasa rayuwarsa yayin da wani ya samu raunauka daga harbin bindiga
  • An ruwaito cewa jami'an 'yan sanda na aikin sintiri ne a yankin Ngbo-Effium lokacin da 'yan bindigar suka kai masu harin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ebonyi - Wani dan sanda ya gamu da ajalinsa a ranar Alhamis a jihar Ebonyi lokacin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta kan tawagar ‘yan sanda da ke sintiri.

Lamarin ya faru ne a yankin Ngbo-Effium, wa da ya dade yana fama da hare-hare a karamar hukumar Ohaukwu.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun sake hana bada kudin fansa idan an yi garkuwa da mutane a Najeriya

Yan bindiga sun kashe jami'in dan sanda a Ebonyi
Yan bindiga sun kashe jami'in dan sanda a Ebonyi. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Joshua Ukandu ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abakaliki, babban birnin jihar, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Wasu ‘yan bindiga sun kai wa jami’an rundunar ‘yan sanda da ke sintiri a kan titin Ngbo-Effium hari ta hanyar amfani da wata mota kirar Toyota Sienna"

Ya ce jami’an ‘yan sandan sun yi artabu da ‘yan ta’addan kuma a fafatawar da suka yi ne daya daga cikin ‘yan sandan ya gamu da ajalinsa.

Ukandu ya kara da cewa wani kuma dan sanda ya samu rauni kuma yanzu haka yana samun kulawa a asibiti.

“Kwamishanan ‘yan sanda na jihar Ebonyi, CP Augustina Ogbodo ya aike da tawagar ‘yan sanda zuwa wurin da abin ya faru.
"Tawagar ta na kan bin diddigin 'yan bindigar yayin da kuma aka dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin", in ji shi."

Kara karanta wannan

Yadda mai garkuwa da mutane ya ba jami’an mu cin hancin naira miliyan 8.5 – ‘Yan sanda

A cewar Joshua Ukandu

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.