Yadda Kaya Suka Yi Mummunan Tashi Watanni 8 da Shigan Tinubu Aso Villa
- Albashin mutane a yanzu bai kai wa ko ina saboda tsabar hauhawar farashin kayayyaki a kasuwanni
- Kayan abinci sun yi tsada tun a lokacin da ake cikin kakar noma, talakawa suna rayuwa a cikin yunwa
- Gwamnatin Bola Tinubu tayi alkawarin gyara tattalin arziki, amma a kullum abubuwa cabewa suke yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Kusan duk inda aka zagaya a Najeriya a halin yanzu, kuka kurum manya da yara suke yi saboda tsabagen tsadar kaya a kasuwa.
Baya ga tsada da ake fama da ita, farashi yana canzawa kamar walkiya. Wani rahoto da aka samu daga Daily Trust ya zo da karin bayani.
Shinkafa, sukari, fulawa sun kara kudi
Shinkafar gida da aka saida buhunta kan N47, 000 a Junairun bara ta zama akalla N58, 000 a Kano, akwai wanda ake saidawa N60, 000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan za a saye shinkafar waje sai an tanadi N70, 000 Buhun fulawa kuwa da ake tunanin ya yi tsada a N35, 000 a bara ya dawo N40, 000.
Wani mazaunin Kano ya shaida cewa buhun sukari ya haura N70, 000 a yau, akwai yiwuwar farashin ya tashi idan watan azumi ya gabato.
Legit ta fahimci kiret na kwai ya zarce N3, 000. Wani ‘dan kasuwa ya ce farashinsu zai tashi saboda tsadar da masara tayi a kasuwa.
Za a saida siminti a kan N3, 500 kuwa?
A ranar Alhamis mu ka samu labari farashin siminti ya kai N7, 000. Wani magini ya shaida mana a N5, 300 ya saye buhun cikin makon jiya.
Rahoton ya ce a Ilorin, baya ga tsadar da simintin ya yi, ya yi wahala. Kwanaki kamfanin BUA ya yi alkawarin maida farashi N3, 5000.
Ma'aikata suna wayyo da tsadar kaya
A manyan garuruwa irin Abuja kuwa, farashin kaya sun wuce haka. Ma’aikatan gwamnati da albashinsu bai canza ba suna wahala.
Gwamnatin tarayya tayi alkawarin biyan N35, 000 duk wata a sakamakon cire tallafin man fetur, sau biyu rak aka taba biyan kudin.
Abinci ya yi tsada a Legas
A kasuwannin Legas kusan babu wani bambancin kwarai tsakanin farashin buhun shinkafa da ta gida yayin da garin tuwo ya kara kudi.
Bokitin wake ya kai N13, 500 tun a yanzu. Wani manomi ya fada mana wakensu bai yi kyau ba a shekarar nan saboda kwari da beraye.
Omokri ya ba Tinubu shawara
Idan Bola Tinubu ya rasa yadda zai magance tashin Dala, ana da labari Reno Omokri ya kawo shawara da za ta iya taimaka masa.
Mukarrabin tsohon shugaban Najeriyan ya kira sunayen wasu, ya ce dole a duba alakar da ke tsakanin NCC da kamfanin MTN.
Asali: Legit.ng