Tashin Hankali Yayin da Mutane Suka Tsere Daga Gidajensu a Jihar Arewa, An Fadi Dalili

Tashin Hankali Yayin da Mutane Suka Tsere Daga Gidajensu a Jihar Arewa, An Fadi Dalili

  • Tsoron harin 'yan bindiga ya sa mutane barin gidajensu a garuruwan Janjala da Gidan Makeri dake karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna
  • Mutanen sun tsere daga gidajensu ne bayan sun hango ayarin 'yan bindiga da yawansu ya kai 100 kan babura
  • Yawancin wadanda suka gudu suka bar gidajen nasu mata da yara ne wadanda ke tsoron kada miyagun su zo su kwashe su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Mazauna garuruwan Janjala da Gidan Makeri da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna sun tsere daga gidajensu bayan hango ayarin 'yan bindiga a kan babura.

An rahoto cewa 'yan bindiga sun farmaki garuruwan a ranar Asabar, inda suka kashe wani bawan Allah da dansa mai shekaru 16 tare da sace wasu 15 a Gidan-Makeri.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da suka sace 'yan makarantar Ekiti sun yi barazanar kashe su

Jama'a na guduwa daga gidajensu a Kaduna
Tashin Hankali Yayin da Mutane Suka Tsere Daga Gidajensu a Jihar Arewa, An Fadi Dalili Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Me ya kori mutane daga gidajensu?

Wani mazaunin garin Janjala, Shuaibu Ibrahim, wanda ya zanta da jaridar Daily Trust ta wayar tarho a ranar Laraba, ya tabbatar da tserewar mutane daga gidajensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim ya ce mazauna yankunan, yawancinsu mata da yara sun gudu sun bar gidajensu tsakanin Asabar da Talata.

Ya ce mutanen sun ci na kare ne a yayin da suka hango 'yan bindigan wadanda yawansu ya kai 100 kan babura.

Jama'a sun shiga rudani

Ya kara da cewar mazauna yankunan sun shiga rudani da suka hango jirgin soji yana kona wani daji da ke kusa da su a karamar hukumar Kachia.

Ya ci gaba da cewa:

"Yanzu haka da nake magana da ku, ina a Kagarko tare da iyalina kasancewar muma mun bar gidanmu a Janjala a ranar Lahadi, amma na ji da safen nan cewa an tura dakarun sojoji yankin a yammacin ranar Talata."

Kara karanta wannan

Mutane da yawa sun mutu yayin da ƴan bindiga suka kai mummunan hari kan bayin Allah a Arewa

Na gudu da iyalina saboda kada a sace mu - Yahaya

Wani mazaunin Janjala, Zubairu Yahaya, wanda shima ya tsere zuwa garin Kagarko tare da iyalinsa, ya ce dole suka bar gida da ahlinsa saboda tsoron kada 'yan bindiga su sace su.

Jaridar ta ruwaito cewa 'yan bindigar, wadanda suka tsere kan baburansu ta daji, sun doshi hanyar Jere.

Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan ba, don baya daukar wayarsa ko amsa sakon da aka aike masa kan ci gaban.

'Yan bindiga sun sace mutane a Neja

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu ƴan bindiga, a wasu hare-hare guda biyu a jiya Talata, sun yi garkuwa da mutum 17 daga garin Garam da kuma ƙauyen Zhibi da ke ƙaramar hukumar Tafa a jihar Neja.

Garam, inda aka yi garkuwa da mutum 14, yana kan hanyar Sabon-Wuse-Bwari, yayin da Zhibi, inda aka yi garkuwa da wasu mutum uku, wani ƙauye ne da ke da iyaka da ƙauyen Dei-Dei, wanda ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bwari ta babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel