Yan Sanda Sun Sake Hana Bada Kudin Fansa Idan An Yi Garkuwa da Mutane a Najeriya

Yan Sanda Sun Sake Hana Bada Kudin Fansa Idan An Yi Garkuwa da Mutane a Najeriya

  • Rundunar 'yan sanda ta gargadi 'yan Najeriya kan biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, ta ce yin hakan kuskure ne
  • Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Fayode Adegoke ya yi wannan gargadin a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba
  • Biyan kudin fansa, a cewar kwamishinan yana sa sana'ar garkuwa da mutane ta bunkasa ba tare da an shawo kanta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Fayode Adegoke, ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.

Biyan kudin fansa, a cewar kwamishinan yana sa sana'ar garkuwa da mutane ta bunkasa, inda ya jaddada cewa "ba a yarda da biyan kudin fansa ba".

Kara karanta wannan

Yadda mai garkuwa da mutane ya ba jami’an mu cin hancin naira miliyan 8.5 – ‘Yan sanda

Ku daina biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, 'yan sanda
Ku daina biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, 'yan sanda sun yi gargadi. Hoto: @LagosPoliceNG
Asali: Twitter

Ya fadi haka ne yayin da yake magana a shirin 'Ra'ayin ku' na TVC a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sace-sacen mutane a cikin birnin Legas

A kwanakin baya, an yi garkuwa da shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Philip Aivoji tare da wasu mutae a hanyar Legas zuwa Ibadan.

Ko a watan Disambar 2023, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wata karamar yarinya mai suna Miracle Adereti, a yankin Ikotun na jihar Legas.

A tsakiyar watan Disamba, 2023, an ce an yi garkuwa da wani shahararren dillalin mota da aka fi sani da Ejike Conversion a cikin kasuwar Ladipo.

Matsayar CP Adegoke kan biyan kudin fansa

Sai dai da yake magana kan biyan kudin fansa, kwamishinan ya ce:

“Batun biyan kudin fansa ba shi da kyau, mutane su daina biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane."

Kara karanta wannan

Yadda ma'aikacin banki ya yi karyar 'yan bindiga sun sace shi saboda bashin naira miliyan 1.7

Da aka tambaye shi game da batun sace-sacen mutane da ake yi a jihar da kuma yadda za a iya kai rahoton rahoton satar mutane, Adegoke ya ce:

“Ba zan yarda da duk wadannan labaran na garkuwa da mutane ba domin ba a kawo mana rahoton wanda ya faru a Gbagada, da na Ago Okota ba.
"Rahoton satar mutanen da kawai muka samu shine wanda aka yi a Idimu kuma mun dauki matakin da ya dace."

Taraba: Mai garkuwa da mutane ya ba 'yan sanda cin hanci

A wani labarin, wani mai garkuwa da mutane da rundunar 'yan sanda ta kama a jihar Taraba, ya ba jami'an rundunar cin hancin naira miliyan 8.5.

An ruwaito cewa ya ba da kudin ne domin jami'an su sake shi ya gudu, sai dai 'yan sandan sun nuna masa muhimmancin kakinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.