'Yan Bindiga Sun Sace Daraktan Babbar Hukumar Gwamnatin Tarayya Kusa da Sansanin Soji a Abuja

'Yan Bindiga Sun Sace Daraktan Babbar Hukumar Gwamnatin Tarayya Kusa da Sansanin Soji a Abuja

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a kusa da wani sansanin soji da ke birnin tarayya Abuja
  • Ƴan bindigan a yayin farmakin, sun yi awon gaba da wani darakta a ma'aikatar kula da gidaje ta tarayya da ke Abuja
  • Harin dai ya firgita mazauna bayan da ƴan bindigan suka riƙa yin harbi ba ƙaƙƙautawa kafin su sace daraktan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A ranar Alhamis wasu ƴan bindiga suka yi awon gaba da wani darakta a hukumar kula da gidaje ta tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja, mai suna Aondo Ver.

Ƴan bindigan sun sace daraktan ne a gidansa, a wani hari da suka kai kimanin mita 200 a kusa da wani sansanin soji da ke Pambara a ƙaramar hukumar Bwari a Abuja, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa kai cikin gida, sun yi garkuwa da ƴan mata 2 a FCT Abuja

'Yan bindiga sun sace darakta a Abuja
'Yan bindiga sun sace darakta a kusa da sansanin soji a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan ta’addan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren ranar Alhamis, inda suka yi ta yi harbi ba kakkautawa, lamarin da ya haifar da firgici a yankin, kafin daga bisani su kutsa cikin daji tare da wanda suka sace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda harin ya auku

Mazauna yankin da suka tabbatarwa jaridar faruwar lamarin a ranar Alhamis sun bayyana cewa, akwai jami’an soji a wani sansanin soji da aka fi sani da ‘camp’, wanda ke da tazarar mita 200 daga inda aka sace daraktan a Pambara Extension.

Sun kuma ƙara da cewa mazauna yankin da ƴan bindiga suka kai wa hari, sun haɗa da jami’an soji da masu aiki da waɗanda suka yi ritaya da kuma fararen hula.

Jaridar Sahara Reporters ta ce ƙoƙarin da ƴan banga suka yi na ceto daraktan bai haifar da ɗa mai ido ba, saboda ba su da makamai masu kyau.

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki muhimmin mataki domin magance matsalar rashin tsaro a jihar Arewa

Wani majiya ya bayyana cewa:

"Ƴan bindiga sun kai hari a Pambara Extension da daddare, da misalin ƙarfe 12:30 na daren yau (Alhamis), inda suka yi awon gaba da wani makwabcinmu, Mista Aondo Ver, wanda darakta ne a hukumar kula da gidaje ta tarayya a Abuja.
"Harin ya afku a kusa da wani sansanin soji da ke ƙofar Bwari kusa da Pambara Extension. Yankin Pambara Extension inda aka yi garkuwa da Mr Ver yana da tazarar mitoci 200 daga sansanin sojin.
"Amma masu garkuwa da mutanen sun tsere ta cikin daji tare da wanda suka sacen."

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ba, saboda bai amsa saƙon da aka tura masa ba kuma bai ɗauki kiran wayar da aka yi masa ba.

Har ila yau, ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh ba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke kasurgumin shugaban ƴan bindiga a Arewa, sun ceto mutum 20 da aka sace

Ƴan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Matar Aure da Ƴaƴanta

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun shiga har cikin gida sun yi awon gaba da wata matar aure da ƴaƴanta a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun sace matar auren ne tare ƴaƴanta bayan mijinta ya ƙi yarda su tafi da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng