'Yan Sanda Sun Cafke Matar da Ke Ƙoƙarin Sayar da Ƴaƴanta Kan N1.8m, Bidiyo Ya Bayyana

'Yan Sanda Sun Cafke Matar da Ke Ƙoƙarin Sayar da Ƴaƴanta Kan N1.8m, Bidiyo Ya Bayyana

  • Gwamnatin jihar Anambra ta kama wata mata mai suna Chinyere Chukwu, mai shekara 38, bisa yunkurin sayar da ƴaƴanta maza biyu
  • Chukwu ta haɗa baki da ɗiyarta mai shekaro 17 don aikata laifin fataucin yara "saboda matsalar tattalin arziki" a Najeriya
  • Ma’aikatar harkokin mata da ƙananan yara ta jihar Anambra ce ta bankaɗo laifin da Chukwu ta aikata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ihiala, jihar Anambra - Ƴan sanda a jihar Anambra sun kama wata mata mai suna Chinyere Chukwu bisa ƙoƙarin sayar da ƴaƴanta maza biyu.

Chukwu, mai shekara 38, an ba da rahoton cewa, ta haɗa baki da ɗiyarta mai shekara 17, Joy, don sayar da ƴaƴanta maza biyu "saboda matsalar tattalin arziki a ƙasar ɓan".

Kara karanta wannan

Majalisa ta dauki muhimmin mataki domin magance matsalar rashin tsaro a jihar Arewa

'Yan sanda sun cafke matar da ke yunkurin sayar da ƴaƴanta a Anambra
Matar ta ce dole ce ta sanya ta yi yunkurin sayar da ƴaƴanta kan N1.8m Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, kwamishinan mata da walwalar jama’a ta jihar, Ify Obinabo, ta jagoranci wasu jami’an tsaro wajen cafke matar mai yara 11 da Joy a daren ranar Talata, 30 ga watan Janairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kama ta, ta ce ta fara sha'awar kasuwancin haram ɗin ne bayan makwabciyarta ta yi nasarar sayar da ɗaya daga cikin ƴaƴanta, cewar jaridar Blueprint.

Sai dai, ƴan sanda sun samu nasarar yin caraf da ita.

Meyasa ta yi yunƙurin sayar da ƴaƴanta?

A kalamanta:

"Ina da yara 11 kuma lokacin da na kasa kula da su, na yanke shawarar sayar da biyu daga cikinsu. Tunda su maza ne aka aka yi musu kuɗi kan N1m kowannensu, amma bayan kwamishina wacce ta yi basaja a matsayin mai saya ta nemi ragi, sai muka yanke shawarar sayar da su a kan N1.8m maimakon N2m da aka amince tun farko.

Kara karanta wannan

Duk da 'yarsa na aiki a CBN, sanatan APC ya caccaki mayar da FAAN, CBN zuwa Legas

"Wannan shine lokaci na farko da na yi yunƙurin irin wannan kasuwancin."

Kalli bidiyon a nan:

Hukumar hana safarar mutane ta ƙasa (NAPTIP) ta sha yin caraf tare da gurfanar da mutanen da ke da hannu wajen sayar da ƙananan yara a yankin Kudu maso Gabas a shekarun baya.

Ƴan Sanda Sun Cafke Mai Sayar da Yara

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta samu nasarar cafke wani mai garkuwa mutane tare da safarar ƙananan yara.

Tayo Adeleke wanda ya daɗe yana tafka wannan ta'asar inda yake kai yaran ƙasar Jamhuriyar Benin yana sayar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng