Tashin Hankali: Mutane 30 Sun Mutu Yayin da Wani Abu Ya Fashe a Jihar APC, Bayanai Sun Fito
- Mutane da yawa sun rasa rayuwarsu a wani yankin da ake haƙo ɗanyen mai Obitti da ke ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema a jihar Imo
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda, Henry Okoye, ya ce an samu fashewa a wurin saboda ayyuka ɓarayin man fetur a Obitti Rubber Estate
- Legit Hausa ta rahoto cewa masu satar mai da dama sun mutu yayin da tankar fetur ya ƙone, kadarori da gonaki suka salwanta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Imo - Rahotanni sun ce kimanin mutane 30 ne suka mutu yayin da aka samu fashewar wani abu a wurin da ake gudanar da aikin haƙo mai a jihar Imo.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, lamarin ya faru ne a dajin Obitti, karamar hukumar Ohaji/Egbema (LGA) ranar Talata, 30 ga watan Janairu.
Har yanzun ba a iya gano bayanan waɗanda suka mutu sakamakon fashewar ba saboda sun ƙone ƙurmus ta yadda ba za a iya gane su ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Tribune ta yi nuni da cewa mutane da da yawa da ba a san adadinsu ba ne lamarin ya rutsa da su, inda aka tafka asarar kadarori da filayen noma na miliyoyin Naira.
Wasu mazauna garin sun tsere daga gidajensu saboda tsoron binciken da mai yiwuwa hukumomin tsaro za su yi a yankin.
Rundunar ƴan sanda ta maida martani
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kogi, ASP Henry Okoye, ya ce an tura tawagar bincike zuwa wurin.
Ya ce tawagar wanda ta kunshi kwararru zata gudanar da bincike da nufin gano ainihin abinda ya haddasa tashin bam ɗin a wurin haƙar man.
Mangu: An kashe bayin Allah 91 yayin da wasu 158 suka ji raunuka a rikicin da ya ɓarke a jihar arewa
Okoye ya kuma yi alƙawarin cewa rundunar ƴan sanda za ta cafke duk mai hannu a wannan lamarin
Amma dangane da adadin mutane da suka mutu kuwa, kakakin ƴan sandan ya ce har yanzun bai sami cikakken bayani ba.
Ƴan bindiga sun sace ƴan mata a Abuja
A wani rahoton kuma Wasu ƴan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun shiga har cikin gida, sun sace ƴan mata 2 ƴan uwan juna a birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa maharan sun yi yunkurin tafiya da ƴan uwa uku amma daga bisani suka sako namijin ya dawo.
Asali: Legit.ng