Dakarun Sojoji Sun Sheke Kasurgumin Shugaban Ƴan Bindiga a Arewa, Sun Ceto Mutum 20 da Aka Sace

Dakarun Sojoji Sun Sheke Kasurgumin Shugaban Ƴan Bindiga a Arewa, Sun Ceto Mutum 20 da Aka Sace

  • Dakarun sojoji masu aikin wanzar da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma sun samu nasarar halaka wani shugaban ƴan ɓindiga a Zamfara
  • Sojojin na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji sun kuma ceto mutim 20 da ƴan bindigan suka sace
  • Nasarar da sojojin suka samu dai ci gaba ne kan ƙoƙarin da suke yi na kakkaɓe ƴan bindigan a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta 'Operation Hadarin Daji' sun kashe wasu ƴan bindiga biyu, tare da kuɓutar da wasu mutum 20 da aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba a Zamfara.

Daga cikin ƴan bindigan da aka kashe har da wani fitaccen shugaban ƴan bindigan mai suna Sainaje daga jihar Katsina a wani samame na daban da sojojin suka kai, cewar rahoton Tvc News.

Kara karanta wannan

Dakarun ƴan sanda sun yi ƙazamin gamurzu da gungun ƴan bindiga, sun samu gagarumar nasara

Sojoji sun sheke shugaban ƴan bindiga
Dakarun sojoji sun yi nasarar halaka shugaban ƴan bindiga a Zamfara Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ Kyaftin Ibrahim Hahaha ya sanyawa hannu, ta ce nasarorin da aka samu ci gaba ne kan aikin da sojojin ke yi domin kakkaɓe ƴan ta'adda a Zamfara da kewaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ina aka kashe ƴan bindigan?

Ya ce an kai harin ne a maɓoyar ƴan bindigan da ke Rukudawa, Dumburum, Tsanu, Birnin Tsaba, Magare da Shamushalle a ƙananan hukumomin Zurmi da Birnin Magaji na jihar Zamfara, rahoton jaridar Nigerian Tribune ya tabbatar.

A yayin farmakin a cewar sanarwar, an lalata dukkan maɓoyar ƴan ta’addan, ciki har da ta wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Sule, yayin da ƴan bindigan suka tsere daga sansanoninsu yayin musayar wuta da sojojin.

Hakazalika, sojojin sun sake ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a lokacin da suke kan hanyar wucewa ta hanyar Shinkafi zuwa Isa a Zamfara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da babban dan kasuwa a jihar Arewa

Waɗanda suka yi garkuwa da su sun yi watsi da su ne a yayin wani artabu da dakarun soji masu ƙwazo wadanda suka ɗauki matakin ceto a kan lokaci.

Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan mutanen da aka ceto an miƙa su ga hukumomin da suka dace domin a haɗa su da iyalansu.

Sojoji Sun Ceto Mutanen da Aka Sace a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar ceto mutum 35 da ƴan bindiga suka sace a jihar Katsina.

Sojojin sun samu wannan nasarar ne bayan sun kai farmaki a maɓoyar ƴan ta'addan da ke cikin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng