Masarauta Ta Yi Fatali da Bukatar Sanatan APC Kan Rushe Masallatai 2, Ta Bayyana Dalilai

Masarauta Ta Yi Fatali da Bukatar Sanatan APC Kan Rushe Masallatai 2, Ta Bayyana Dalilai

  • Rikicin siyasar Goje da Kumo ta sauya salo bayan bukatar rushe masallatan Pindiga da Tumu da Sanatan ya yi
  • Sai dai Masarautar Pindiga a karamar Akko da ke Gombe ta yi fatali da bukatar Sanata Danjuma Goje
  • Legit Hausa ta tattauna da jigon jam'iyyar APC a yankin mazabar Akko kan wannan lamari

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Masarautar Pindiga a karamar Akko da ke jihar Gombe ta yi fatali da bukatar Sanata Danjuma Goje.

Masarautar ta ki amincewa da bukatar Sanatan don rushe masallatan Pindiga da Tumu don gyara su, cewar Punch.

Masarauta ta yi fatali da bukatar Sanatan APC kan rushe masallatai
An yi watsi da bukatar Goje kan rushe masallatai 2. Hoto: Senator Danjuma Goje.
Asali: Twitter

Mene Goje ke bukata da masallatan?

Goje wanda ke wakiltar Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya bukaci hakan ne bayan sabunta masallatan shekaru uku da suka wuce.

Kara karanta wannan

Sun fi na Buhari, Shehu Sani ya fadi abin da ya kamata a yi wa hafsoshin tsaro, ya shawarci mutane

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abokin hamayyarsa a siyasa, Usman Bello Kumo shi ya gyara su a yankin shekaru uku da suke wuce.

Kumo shi ke wakiltar mazabar Akko a Majalisar Wakilai wanda tun asali yaron Sanatan ne a siyasa, cewar Leadership.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren Masarautar, Mohammed Audi ya fitar a jiya Talata 30 ga watan Janairu.

Audi ya ce masarautar ta yi zama da masu ruwa da tsaki da wasu 'yan siyasa kan lamarin kuma dukkansu sun yi fatali da bukatar.

Ya ce sun tabbatar da cewa masallatan biyu na cikin yanayi mai kyau wanda ba su bukatar wata gyara ko rusawa, cewar Sahara Reporters

Sun bukaci Sanata Goje ya gudanar da wasu ayyukan ci gaba ba a yankunan biyu ba sai dole gyaran masallatan ba.

Martanin masarautar kan bukatar Goje

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamna Abba Kabir ya yi martani kan yarjejeniyarsu da Tinubu don komawa APC, ya yi godiya

Sanarwar ta ce:

"Masarautar Pindiga ta na samar da jama'a cewa a ranar Litinin 29 ga watan Janairu ta yi zaman da masu ruwa da tsaki kan jita-jitar rusa masallatan Pindiga da Tumu da Sanata Danjuma Goje ke shirin yi.
"Kowa ya amince cewa dukkan masallatan suna da kyau ba su bukatar gyara ko rusawa, duk mai neman kawo ci gaba a yankunan akwai hanyoyi da yawa da suke bukata.
"Cikin ladabi da girmamawa, muna sanar da hukumomi cewa wannan shi ne matsayar mu kuma mun ki amincewa da bukatar Sanata Goje na rushe masallatan Pindiga da Tumu a yanzu."

Legit Hausa ta ji ta bakin jigon APC a yankin, Hon. Muhammad Auwal Akko kan lamarin.

Hon. Akko ya ce madadin rusa masallatan ya kamata a inganta rayuwar mabukata ta wasu hanyoyi.

Ya ce:

"Madadin a rusa wadannan masallatai da ba su da matsala, kamata ya yi a inganta wasu matsaloli ko kuma ayi wa mabukata, tunda akwai wurare da dama da suke da bukata."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe matar ɗan sanda da surukarsa a wata jihar Arewa

Kotun Koli ta yi hukunci a zaben Gombe

Kun ji cewa Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Gwamna Inuwa Yahaya a matsayin gwamnan Gombe.

Har ila yau, kotun ta yi watsi da karar dan takarar jam'iyyar PDP, Jibrin Barde saboda rashin hujjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.