Alhaki: Bayan fashin mota, ya yi hadari ya mutu a ciki garin tserewa

Alhaki: Bayan fashin mota, ya yi hadari ya mutu a ciki garin tserewa

Wani dan fashi da ya sace mota kirar Toyota Highlander daga hannun wata Hajiya Aisha Abdullahi a jihar Katsina ya haddu da ajalinsa a yayin da yake kokarin tserewa da motar da ya sace bayan ya yi hatsari.

Kwamishinan yan sandan jihar, Mohammed Wakil ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a jiya inda ya ce wanda ake zargi da aikata fashi da makamin ya mutu sakamakon hatsarin.

Wakil ya kara da cewa hukumar yan sanda ta kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu cikin aikata fashin .

Alhaki: Bayan fashin mota, ya yi hadari ya mutu a ciki garin tserewa
Alhaki: Bayan fashin mota, ya yi hadari ya mutu a ciki garin tserewa

DUBA WANNAN: APC na matsa min na sayar masu da tikitin takarar PDP - Fayose

Wadanda aka kama sune Sanusi Abdullahi mai shekaru 22 wanda akafi sani da Saga da Mansur Abdullahi mai shekaru 21 wanda akafi sani da Washa sai Aliyu Salisu mai shekaru 22 wanda akafi sani da Alious kuma duk mazauna Katsina ne.

A cewar kwamishinan, "A ranar 27 ga watan Yuni misalin karfe 7.45 na yamma an sanar da yan sandan Sabon Gari cewa yan fashi sun kaiwa wata Hajiya Aisha Abdullahi hari a gidanta dake Sabuwar Unguwa Quaters a Katsina.

"Sun sace mata motarta kira Toyota Highlander 2003 mai kalar ruwan toka da kuma lamba AS 579 KTS.

"Yan sandan sun nufi gidanta amma sai suka gano motar a hanya tayi hatsari kusa da masallacin GRA a Katsina ciki kuma da gawar wani da ake kyautata zaton daya daga cikin yan fashin ne.

"Bayan an gano ko gawar wanene sai akayi amfani da bayanan aka gano sauran mutane ukun da ke zargin sunyi fashin tare."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel