N200,000 Tayi Kadan: ‘Yan Kwadago Sun Yanke Albashin da Suke So a Koma Biyan Ma’aikata

N200,000 Tayi Kadan: ‘Yan Kwadago Sun Yanke Albashin da Suke So a Koma Biyan Ma’aikata

  • Kungiyoyin kwadago da na ‘yan kasuwa sun bayyana ra’ayinsu a game da batun karin albashi
  • Shugabannin TUC suna so mafi karancin albashi ya zama $300 wanda a yanzu ya haura N250, 000
  • Kungiyar NLC ta janye maganar N200, 000 a matsayin akallan albashi, tana ganin ba zai isa ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A yayin da aka fara tattaunawa domin ganin an yi wa ma’aikata karin albashi, ‘yan kwadago sun gabatar da shawararsu.

Tribune ta rahoto shugabannin ma’aikatan suna cewa ba za ta yiwu a rayu a kan N30, 000 da Muhammadu Buhari ya kawo a 2019 ba.

Albashi
Kwamitin karin albashi Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Ma'aikata na neman albashin $300 a wata

Kungiyoyin kwadago sun yanke $300 a matsayin mafi karancin albashin da ya kamata ma’aikaci ya karba kowae wata a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fara shirin kara albashin ma’aikata, an sa ranar kafa kwamiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma’aikata suna kukan cewa tsadar rayuwa, janye tallafin man fetur da karyewar Naira ya jawo albashin da ake biya bai iya rike mutum.

Shugaban bangaren ‘yan kasuwa a majalisar JNPSNC, Kwamred Benjamin Anthony ya gabatar da ra’ayinsu a ranar Talatar nan a Lafiya.

Albashin ma'aikata ya yi kadan

A wajen wani zama da aka yi Kwamred Benjamin Anthony ya nuna akwai bukatar albashi ya kai akalla $300 kimanin N270, 000 kenan.

Kwamred Boma Mohammed wanda ya wakilci jagoran ‘yan kasuwan ya koka game da bata lokacin da ake yi a wajen biyan albashi.

Da yake bayani, Kwamred din ya ce idan mutum ya je kasuwa yanzu da N100, 000, da leda guda zai dawo gida saboda tashin farashi.

NLC ta janye maganar albashin N200, 000

Ita kungiyar NLC ta ce N200, 000 da ake tunani zai iya zama mafi karancin albashi ya yi kadan, dole gwamnati ta sake yin wani nazarin.

Kara karanta wannan

Yadda wasu suka nemi amfani da kotu a karbe kujerar Abba a Kano Inji Kakakin NNPP

Mataimakin shugaban kungiyar kwadagon na kasa, Tommy Etim ya shaidawa Punch cewa abubuwa sun kara tsanani a yanzu.

Etim ya yi magana ne bayan Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin karin albashi, yake cewa an kara karya darajar Naira.

Ita NLC ba ta yanke wani albashi ba, amma ta ce tabbas N200, 000 ya yi kadan a yau.

Su wanene a kwamitin karin albashi?

Kuna da labari kwamitin karin albashi da aka rantsar ya kunshi bangaren gwamnati da ‘yan kwadago da sauran wakilan ma’aikata.

A kwamitin akwai wakilan gwamnonin shiyyoyi 6 da ‘yan kasuwa daga kungiyoyi dabam-dabam, wadanda babu su ne ‘yan fansho.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng