Tashin Hankali Yayin da Gwamnan PDP Ya Sanya Dokar Hana Fita, Bayanai Sun Fito
- An samu ɓarkewar rikici a tsakanin ƙauyukan Ilobu da Ifon na jihar Osun a ranar Litinin, 29 ga watan Janairu
- Sabon rikicin wanda ya ɓarke a tsakanin ƙauyukan biyu ya sanya Gwamna Adeleke na jihar sanya dokar hana fita a ƙauyukan
- Rikicin dai wanda ya ɓarke ya jawo asarar rayukan mutum biyu yayin da ƴan sanda suka cafke wasu mutum da ake zargi akwai hannunsu a rikicin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake sanya dokar hana fita daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa karfe 6:00 na safe a ƙauyukan Ilobu da Ifon, biyo bayan sabon rikici da ya ɓarke a garuruwan.
Ya kuma kafa rundunar haɗin gwiwa tare da tura jami’an tsaro ciki har da sojoji zuwa ƙauyukan da a ke rikicin, cewar rahoton The Punch.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Kolapo Alimi, ya fitar ranar Talata, 30 ga watan Janairun 2024, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka sanya dokar hana fitan?
Ƴan bindiga daga ƙauyukan Ilobu da Ifon sun sake fafatawa a ƙauyukan waɗanda ke kan iyakar jihohin Osun da Oyo a ranar Litinin.
Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum biyu tare da lalata dukiyoyi a rikicin da ya ɓarke.
Kafin rikicin baya-bayan nan dai, Adeleke a watan Oktoban shekarar da ta gabata ya sanya dokar hana fita a tsakanin ƙauyukan biyu bayan ɓarkewar ƙazamin rikici.
Sai dai an dage dokar hana fitan a watan Disamba bayan dawowar zaman lafiya a yankin.
Sai dai a ranar Litinin rikici ya sake ɓarkewa, lamarin da ya sa mazauna yankin da dama suka tsere.
Ƴan sanda sun yi kame
A halin da ake ciki, rundunar ƴan sandan jihar Osun ta ce jami’anta sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a rikicin da ya ɓarke tsakanin Ifon da Ilobu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Yemisi Opalola, ya fitar, yayin da yake kira da a kwantar da hankula, ta ce an tura jami’an tsaro a yankin domin dawo da zaman lafiya.
Gwamnan Plateau Ya Sa Dokar Hana Fita
A baya rahoto ya zo cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanya dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.
Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan sabon rikicin da ya ɓarke a ƙaramar hukumar.
Asali: Legit.ng