Sanata Sani Ya Yi Magana Yayin da 'Yan Bindiga Suka Halaka Sarakuna 2 a Jihar APC
- Tsohon dan majalisar tarayya, Sanata Shehu Sani, ya yi Allah wadai da kisan sarakunan gargajiya guda biyu a jihar Ekiti
- Legit Hausa ta rahoto cewa an kashe Onimojo na Imojo-Ekiti, Oba Olatunde Samuel Olusola, da Elesun na Esun-Ekiti, Oba David Babatunde Ogunsola, a ranar Litinin 29 ga watan Janairu
- A cikin wata sanarwa, Sani ya nuna alhininsa kan abun da ya kira da "kisan gilla" sannan ya ce dole a hukunta masu laifin ba tare da an bari sun tsere ma doka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Ado Ekiti, jihar Ekiti - Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani, ya yi martani a kan kisan sarakuna biyu da wasu 'yan bindiga suka yi a jihar Ekiti.
A martaninsa a ranar Talata, 30 ga watan Janairu, Sani ya ce dole a hukunta wadanda suka hallaka sarakunan.
Jaridar Legit Hausa ta rahoto labarin kisan sarakunan a jihar Ekiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya yi Allah wadai da kisan sarakuna a Ekiti
Zuwa yanzu babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin wannan mummunan aika-aika.
A jawabin da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) Sani, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki kuma na Allah wadai.
Jigon na PDP ya rubuta:
"Kisan gillar da aka yi wa sarakunan Ekiti biyu Oba David Babatunde Ogunsola da Oba Olatude Samuel Olusola abun bakin ciki, takaici da Allah wadai ne.
“Dole ne a hukunta wadanda suka aikata laifin. Ina mika ta'aziyyata ga gwamnati da al'ummar jihar Ekiti. Allah ya jikan su da rahama.”
'Dan majalisa ya zub da hawaye
A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa wani ɗan majalisar wakilan Najeriya ya fashe da kuka a ranar Talata a zauren majalisar yayin da yake magana kan matsalar rashin tsaro a jiharsa.
Duk da yake matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara a fadin ƙasar nan, inda kusan kullum ake samun rahotannin kashe-kashe da garkuwa da mutane, ɗan majalisar ya mayar da hankali ne kan sabon lamarin da ya faru a jiharsa.
Asali: Legit.ng