Shettima Ya Kaddamar da Kwamitin Mutum 36 da Za Suyi Aikin Kara Albashin Ma’aikata
- Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin mutum 36 da zai yi aikin kara albashi ga ma'aikata
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Talata a fadar shugaba kasa
- Ana sa ran kwamitin zai ba gwamnati shawarar adadin kudin da ya kamata ya zama mafi karancin albashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Gwamnatin tarayya karshin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta kaddamar da kwamitin mutane 37 da zai yi aiki don kara mafi karancin albashi na ma'aikatan kasar.
The Cable ta ruwaito cewa kwamitin yana da alhakin ba da shawarar sabon mafi karancin albashi da ya kamata gwamnati ta rinka biyan ma’aikatan Najeriya.
Yayin kaddamar da kwamitin a ranar Talata a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci kwamitin da ya gaggauta cimma matsaya tare da mika rahotonsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen da mambobin kwamitin ya kunsa
Mataimakin shugaban kasar ya ce taron ya sake jaddada alkawarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na inganta jin dadin ma’aikatan Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Shettima ya jaddada bukatar bin ka'idojin da aka kafa kwamitin akan su sannan kuma ya bukaci mambobin kwamitin su fadada bincike yayin aikin.
Kwamitin ya kunshi wakilan gwamnatin tarayya da na jihohi, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago, kuma tsohon shugaban ma’aikatan tarayya Bukar Goni Aji ne zai jagoranta.
Mambobin gwamnatin tarayya sun hada da:
- Nkeiruka Onyejeocha, karamar ministar kwadago da samar da ayyuka (wakiltan ministan kwadago da ayyuka);
- Wale Edun, ministan kudi kuma ministan tattalin arziki;
- Atiku Bagudu, ministan kasafin kudi da tsare-tsare.
- Folashade Yemi-Esan, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya;
- Maurice Mbaeri, sakatare na dindindin, ofishin manyan ayyuka (GSO) OSGF; da
- Ekpo Nta, shugaban hukumar albashi, kudaden shiga da albashi na kasa (NSIWC).
Mambobin gwamnatin jihohi sun hada da:
- Mohammed Bago, gwamnan Niger;
- Bala Mohammed, gwamnan Bauchi;
- Umar Radda, gwamnan Katsina;
- Charles Soludo, gwamnan Anambra;
- Ademola Adeleke na jihar Osun; da
- Bassey Otu na jihar Cross River.
Mambobin kungiyar kwadago sun hada da:
- Joe Ajaero, shugaban NLC;
- Emmanuel Ugboaja;
- Adeyanju Adewale;
- Ambali Olatunji;
- Benjamin Anthony da
- Theophilius Ndukuba.
Mambobin kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya (TUC):
- Festus Osifo, shugaban kungiya;
- Tommy Okon, mataimakin shugaba na kasa I;
- Kayode Alakija, mataimakin shugaba na kasa II;
- Jimoh Oyibo, mataimakin shugaba na kasa III.
- Nuhu Toro, babban sakatare; da
- Hafsatu Shuaib, shugabar hukumar mata.
Kungiyar tuntubar ma’aikata ta Najeriya (NECA):
- Adewale-Smatt Oyerinde, babban daraktanta;
- Chuma Nwankwo; da
- Thompson Akpabio.
Mambobin kungiyar 'yan kasuwa, masana'antu (NACCIMA):
- Michael Olawale-Cole, shugaban kungiyar na kasa;
- Ahmed Rabiu, mataimakin shugaba na kasa; da
- Humphrey Ngonadi (NPOM), shugaban rayuwa na kasa.
Membobin kungiyar NASME:
Abdulrashid Yerima, shugaba; da
Theophilus Okwuchukwu.
Mambobin kungiyar masu masana'antu (MAN):
- Grace Omo-Lamai, daraktan kula da ma'aikata na masana'antar ta Najeriya;
- Segun Ajayi-Kadir, darakta-janar na MAN;
- Ada Chukwudozie, Manajan Darakta na Dozzy Oil and Gas Limited.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin, ya bayyana kwarin gwiwar cewa za su yi adalci wajen gudanar da aikin bisa la’akari da tarin mutanen da aka tara.
Bauchi: Mata hudu sun mutu wajen hakar ma'adanai
A wani labarin, akalla mata hudu ne suka mutu bayan da kasa ta rufta kansu yayin da suke hakar ma'adanai a jihar Bauchi.
An ruwaito cewa kasar wajen ta zabtare ta fada kansu kuma an gaza ceto su, lamarin da ya zama silar ajalinsu.
Asali: Legit.ng