Kaduna: Wadanda Suka Yi Garkuwa da Wata Likita da Mijinta Sun Nemi N100m, Sun Yi Barazanar Kisa
- 'Yan bindigar da suka yi garkuwa da wata likita da mijinta a jihar Kaduna sun nemi naira miliyan 100 kudin fansa ko su kashe ma'auratan
- Rahotanni sun bayyana cewa wata guda ke nan ma'auratan tare da wani karamin yaro da ke zaune da su ke a hannun masu garkuwan
- Yan bindigar sun ki karbar naira miliyan 20 da iyalan ma'auratan suka iya haɗawa, sun dage kan naira miliyan 100
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kaduna - Masu garkuwa da suka sace wata likitar ido, Ganiya Olawale-Popoola da mijinta Nuruddeen Popola da wani bakon su, AbdulMuhniy Folaranmi sun nemi naira miliyan 100 kudin fansa.
Wata guda kenan da masu garkuwar suka sace mutanen uku a rukunin gidaje na cibiyar asibitin ido ta kasa da ke karamar hukumar Igabi, a jihar Kaduna.
Jaridar Punch ta tattaro cewa wani daga cikin iyalan ma'auratan ya ce masu garkuwar sun ki yin sassauci kan naira miliyan 100 da suka nema.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baranar da masu garkuwan suka yi
A ranar 27 ga watan Disamba, 2023 ne rahotanni suka bayyana cewa 'yan bindigar sun je har gidan ma'auratan suka sace su, tare da wani karamin yaro da ke zama da su.
Har sai a kwana na hudu ne 'yan bindigar suka kira waya, inda suka bukaci naira miliyan 100 kafin su saki likitar da mijinta wanda jami'in sojan sama ne, da karamin yaron.
Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwan sun yi barazanar kashe ma'auratan idan har ba a biya kudin fansar ba zuwa ranar 18 ga watan Janairu.
Masu garkuwan sun ki karbar naira miliyan 20
Sai dai majiya daga iyalan ma'auratan ya shaida cewa a ranar Juma'a 'yan bindigar sun kira waya tare da maimaita barazanar na cewa za su kashe mutanen idan ba a biya naira miliyan 100 ba.
Ya ce:
"Mun roke su akan su karbi naira miliyan 20 wanda iyalan suka iya haɗawa amma sun ki yarda."
Ko da aka tuntubi kakakin rundunar'yan sanda na jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya ce jami'an tsaro na aiki tukuru don ceto ma'auratan ba tare da wani abu ya same su ba.
Yan bindiga sun tare mota, sun sace yara 'yan makaranta
A wani labarin kuma, yan bindiga sun sace wasu yara 'yan makaranta a karamar hukumar Emure da ke jihar Ekiti.
Hakan na zuwa kwanaki kadan bayan da yan bindiga suka kashe wasu manyan sarakunan gargajiya biyu a jihar.
Asali: Legit.ng