Satar Basarake: Masu garkuwa da mutane sun nemi Naira 100 miliyan kudin fansa
Maharan da suka sace Basaraken Agwam Akulu, Kukah sun nemi a biya Naira milyan 100 a matsayin kudin fansa kafin su sake shi.
A ranar Talata da ta gabata ne dai, maharan suka kai farmaki kauyen Akulu inda suka rika harba bindigogi kafin daga baya su arce da basaraken da kuma daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.
KU KARANTA: An sace alkalin wata kotu a Neje
Legit.ng haka zalika ta samu cewa tsohon mai baiwa gwamnan Taraba shawara kan harkokin siyasa, Mista Adamu Kwanci ya karbi musulunci.
Mista Kwanci ya ce bai yanke shawarar shiga addinin Musulunci ba sai da ya gudanar da bincike da dogon nazari, sannan karshen lamari ya gane cewar Musulunci shine Addinin gaskiya, sannan Musulmi sune jama'ar da su ka fi kowa son zama lafiya da tausayi.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng