Jerin Sunayen 'Yan Kwamitin Mutum 36 da Za Suyi Aikin Kara Albashin Ma'aikata

Jerin Sunayen 'Yan Kwamitin Mutum 36 da Za Suyi Aikin Kara Albashin Ma'aikata

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi na’am da kafa kwamiti na musamman a kan batun karin albashi a Najeriya
  • ‘Yan kwamitin za su duba lamarin albashin ma’aikata, su kawo shawarar abin da ya dace a kara masu
  • Bukar Goni Aji zai jagoranci kwamitin na Shugaban kasa mai dauke da ministoci da ‘yan kwadago

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - An zakulo ‘yan kwamitin karin albashin ne daga jami’an gwamnatin tarayya da na gwamnatocin jihohi da bangaren ‘yan kasuwa.

A kwamitin akwai kungiyoyin kwadago da suka huro wuta cewa sai an yi karin albashi tun da aka janye tallafin fetur a shekarar bara.

Bola Tinubu
Bola Tinubu zai kara albashi Hoto: @AjuriNgelale da @Dolusegun16
Asali: Twitter

Kwamitin na Bukar Aji Goni ya cika. The Nation tace wadanda babu a ciki su ne ‘yan fansho watau tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Jerin sunayen attajiran Najeriya 40 da suka mallaki jiragen sama na alfarma da yawan kudadensu

Hadimin shugaban kasa, Olusegun Dada ya jero 'yan kwamitin a shafinsa na X.

Su wanene 'yan kwamitin karin albashi?

Wakilan gwamnatin tarayya

1. Nkeiruka Onyejeocha

2. Mista Wale Edun

3. Alhaji Atiku Bagudu

4. Yemi Esan

5. Dr. Nnamdi Maurice Mbaeri

6. Ekpo Nta, Esq.

Bangaren gwamnatocin jihohi

Waklai daga gwamnoni 6:

7. Alh. Mohammed Umar Bago

8. Sen. Bala Mohammed

9. Alh. Umar Dikko Radda

10. Farfesa Charles Soludo

11. Sen. Ademola Adeleke

12. Mista Otu Bassey Edet

Kungiyoyin ma’aikata

Legit ta fahimci an dauko wakilai daga kungiyoyin NACCIMA, NECA, NPOM da NASME.

13. Adewale-Smatt Oyerinde

14. Mista Chuma Nwankwo

15. Mista Thompson Akpabio

16. Asiwaju (Dr) Michael Olawale-Cole

17. Hon. (Dr) Ahmed Rabiu

18. Cif Humphrey Ngonadi

19. Dr. Abdulrashid Yerima

20. Hon. Theophilus Nnorom Okwuchukwu

Bangaren kasuwa

A nan akwai wakilai daga masu manyan kamfanoni, harkar mai da ‘yan kungiyar MAN

21. Dr. Muhammed Nura Bello

22. Misis Grace Omo-Lamai

23. Segun Ajayi-Kadir

24. Lady Ada Chukwudozie

Kungiyoyin kwadago

Gwamnatin tarayya ta kawo ‘yan kungiyoyin kwadago da na ‘yan kasuwa a kwamitin:

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da za su faru da NNPP da APC idan Abba, Kwankwaso suka sauya-sheka

25. Kwamred Joe Ajaero

26. Kwamred Emmanuel Ugboaja

27. Kwamred Prince Adeyanju Adewale

28. Kwamred Ambali Akeem Olatunji

29. Kwamred Benjamin Anthony

30. Farfesa Theophilius Ndukuba.

31. Kwamred Festus Osifo

32. Kwamred Tommy Etim Okon, PhD,

33. Kwamred Kayode Surajudeen Alakija

34. Kwamred Jimoh Oyibo

35. Kwamred Nuhu A. Toro,

36. Kwamred Hafusatu Shuaib

Za a kaddamar da kwamitin albashi

Rahoto ya zo a baya cewa Sanata George Akume ya sanar da za a rantsar da kwamitin karin albashi a fadar Aso Rock a yau Talata.

Sakataren gwamnatin tarayya ya ce za a kaddamar da kwamitin yayin da Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa a makon da ya wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng