Dala Ta Lula N1400, CBN Ya Dauki Mataki Domin a Tsira da Ragowar Darajar Naira

Dala Ta Lula N1400, CBN Ya Dauki Mataki Domin a Tsira da Ragowar Darajar Naira

  • Babban bankin Najeriya ya narka kudi a kasuwar canji domin a samu saukin tsadar Dalar Amurka
  • Sanarwa ta fito cewa an ware wasu $500m domin biyan bashin da suka taru daga cinikin ketare
  • Ana sa ran idan aka kammala biyan wadannan kudi, Dala ta samu ta yadda darajar Naira za ta karu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Babban bankin Najeriya na CBN yace ya saki $500m ga bangarori dabam-dabam yayin da farashin Dala ya harba sama.

CBN ya saki dalolin ne domin biyan bashin da aka tara daga cinikin kudin kasashen waje, The Cable ta fitar da wannan labari a yau.

Dala.
CBN: Dala $1 ta kai N1450 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

CBN yana biyan tsofaffin bashi

Akwai wadanda aka tabbata sun yi ciniki da kudin waje, an dauki lokaci ba a biya su kudinsu ba, sai yanzu CBN ta ke sauke nauyin.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari sun jawo za a binciki inda Gwamnoni 150 da Ministoci Suka Kai N40tr

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan yana zuwa ne kwanaki kadan bayan an ji cewa babban bankin ya batar da Dala biliyan 2 a bangarorin jiragen sama da mai.

Shugabar harkokin sadarwa ta rikon kwarya a CBN, Hakama Sidi-Ali, ta bada wannan sanarwa a garin Abuja a safiyar Litinin.

Dabarar da gwamnan CBN ya kawo

Hakama Sidi-Ali tace hikimar hakan ita ce CBN ya sauke nauyin duk wani bashin cinikin kudin kasar waje cikin kankanin lokaci.

Sabon gwamnan bankin CBN da aka nada, Yemi Cardoso ya dage wajen ganin an samar da kudin kasahen waje a kasuwar canji.

Burin Cardoso shi ne a daina fama da karancin Dala wanda hakan ya jawo tashin farashinsa.

Sidi-Ali tace gyare-gyaren da aka kawo za su tabbata wajen ganin an samu sauyin da aka dade ba a gani ba a kasuwar canjin kudi.

Kara karanta wannan

An kama 1 daga kasurguman 'yan bindigan da suka sace Nabeeha da 'yan uwanta a Abuja

An rahoto shugabar sadarwar tana mai cewa an daidaita kasuwar canji tare da tabbatar da gaskiya wajen cinikin kudin kasar waje.

Idan Naira tayi karfi, Sidi-Ali tace ‘yan kasuwa za su kawo hannun jari daga kasashe, abin da gwamnati mai-ci ta ke ta kokarin yi.

Jerin masu kudin Duniya

Kun ji labari ana lissafin arzikin Bernand Arnault mai shekara 74 da ‘yan zuri’arsa ya haura Dala biliyan 207, sun sha gaban Elon Musk.

Idan aka tambaye ka wanene wanda ya fi kowa kudi, to amsar ba za ta kasance Elon Musk ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng