Jihar Borno Zata Ginawa Yan Gudun Hijira Gidaje 20,000 Kauyuka 3

Jihar Borno Zata Ginawa Yan Gudun Hijira Gidaje 20,000 Kauyuka 3

  • Jihar Borno na fama da yan gudun hijira tun daga 2014 zuwa yau sakamakon ayyukan book haram masu ikirarin jihadi
  • Yakin na Boko haram ya daidaita mazauna garin Borno da kewaye inda suka fantsama kasashe daban daban don tsira da ransu
  • Gwamnatin Borno a kokarin ta na dawo dasu gida, tana kokarin gina gidaje 20, 000 da kauyuka guda 3

Borno - Gwamaan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya zayyana wani shiri da ake domin tsugunar da yan gudun hijiran da rigimar Boko Haram ta 'dai'daita tun a 2014.

Akalla yan gudun hijira guda 20, 000 ne suka rasa mazaunan su sakamakon ayyukan kungiyar a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Wannan rashin na gidaje shine daliline da yasa yan gudun hijrar suka shiga makwabtan Najeriya irin su Chadi, Kamaru da Nijer.

Kara karanta wannan

Madalla: Buhari ya amince a ba Zulum N15bn don yin wani babban aiki a Borno

Gwamna Zulum
Jihar Borno Zata Ginawa Yan Gudun Hijira Gidaje 20,000 Kauyuka 3 Hoto: Legit.ng
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar Leadership ta ruwaito Zulum na fadin haka a yayin da yake jagorantar kwamitin da aka daurawa alhakin gudanar da aikin a ofishin jihar Barno da yake Abuja, a Litinin din da ta gabata.

Zulum dai shine Mataimakin Shugaban Kwamitin dake kula da kara tsugunar da yan gudun hijirah da kuma kula da tubabbun yan kungiyar Boko Haram, inda mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo ke zama Shugaban Kwamatin.

Gwamnan yace, Shugaban Kasa Buhari ya amince da’a zari kudi Naira Biliyan 15 a damkawa kwamitin, tare da gwamnatin Borno a matsayin mai kula da aikin na sake gina kauyuka 3 domin dawo dasu gida. Rahoton Vanguard.

Zulum yace, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce zata kula da bangaren samar da abinci da kayan yau da gobe domin tattara lamurran yan gudun hijrar daga kasashen Chadi, Kamaru da jamhuriyyar Nijer, kamar yadda jaridar Pulse.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Dama Na Faɗa" Gwamna Wike Ya Maida Martanin Kan Maye Gurbin Shugaban PDP Na Kasa

A Sake Duba Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kaduna – Masu Saka Ido Ga INEC

Gamayyar masu sanya ido akan zaben Najjeriya sunyi kira ga hukumar zabe ta kasa data kara duba na tsanaki ga sakamakon zaben jihar Kaduna.

Hakan na cikin wani rahoto da jaridar Legit.ng ta ruwaito, inda masu sanya idon sukace anyi zabe cikin nasara, amma wajen tattara sakamakon zabe an samu gagarumara matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel