'Yan Bindiga Sun Tafka Ta'asa a Zamfara, Sun Yi Awon Gaba da Amarya da Ango

'Yan Bindiga Sun Tafka Ta'asa a Zamfara, Sun Yi Awon Gaba da Amarya da Ango

  • An shiga jimami bayan wani sabon harin da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara
  • Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai a ƙauyen Madabanciya sun yi awon gaba da wasu ma'aurata sabon aure
  • Mazauna yankin sun miƙa kokensu ga hukumomi da su kai musu jami'an tsaro yankin domin kare su daga farmakin ƴan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Madabanciya da ke ƙaramar hukumar Bungudu a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da wasu miji da mata sabon aure.

Wani ɗan yankin mai suna Ibrahim Sani ya ce ƴan bindigan sun isa ƙauyen ne da ƙafa da misalin ƙarfe 11:45 na daren ranar Lahadi, inda suka bar baburansu a wajen ƙauyen.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da babban dan kasuwa a jihar Arewa

Yan bindiga sun sace amarya da ango a Zamfara
Yan bindiga sun sace amarya da ango a jihar Zamfara Hoto: @Mfarees
Asali: Twitter

Sani ya ce ƴan bindigan da suke da yawa suna riƙe da manyan makamai ne, inda suka fara harbe-harbe nan take bayan sun isa ƙauyen, don tsoratar da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ƴan bindigan sun riƙa bi gida-gida suna neman kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja, rahoton Eagleonline ya tabbatar.

Ƴan bindigan sun sace kayayyaki masu yawa

Ya ƙara da cewa:

"Sun yi awon gaba da dabbobi masu yawa da kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.
"Suna cikin zagayawa a ƙauyen, sai suka ci karo da wasu ma'aurata sabon aure inda suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji."

Sani ya ce babu wani jami’in tsaro da ke aiki a ƙauyen don kare rayuka da dukiyoyin al’umma, duk kuwa da ƙalubalen tsaro da ke addabar jihar.

Ya yi kira ga hukumomi da su tura jami’an tsaro yankin, inda ya kammala da cewa “idan ba a yi wani abu a kan lokaci ba, za a bar mu da ba mu da wani zaɓi da ya wuce mu koma wasu wurare."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun nemi makudan kudin fansa kan mutum 31 da suka sace a Arewa, sun tura da sako

Ba samu jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗan Kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun sace wani babban ɗan kasuwa a jihar Sokoto.

Ƴan bindigan dai sun sace ɗan kasuwan ne bayan wani hari da suka kai cikin ƙaramar hukumar Tambuwal ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng