Magoya Bayan APC Sun Yi Wa Hadimin Akpabio Tsinannen Duka Har Lahira Kan Dalili 1, Bayanai Sun Fito
- Ana zargin shugabannin jam’iyyar APC da daukar nauyin kisan hadimin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio
- Marigayin Ime Udoworen ya gamu da tsautsayin ne bayan zargin ya handame kayayyakin da aka bayar don rabawa
- Iyalan marigayin sun bukaci Sifetan ‘yan sanda ya nemo musu gawar dan nasu wanda har yanzu ba a san inda ta ke ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom – Wasu matasa sun hallaka hadimin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan rabon kayan Kirsimeti.
Marigayin Ime Udoworen ya gamu da tsautsayin ne bayan an yi zargin ya handame kayayyakin da aka bayar don rabawa.
Mene ake zargin jigon APC da shi?
Ana zargin shugabannin jam’iyyar ce suka dauki nauyin wasu matasa inda suka masa dukan tsiya har sai da ya mutu kan zargin lamushe kayan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Iyalan marigayin sun bukaci Sifetan ‘yan sanda ya nemo musu gawar dan nasu wanda har yanzu ba a san inda ta ke ba.
Ime kafin rasuwarshi shi ne shugaban matasan jam’iyyar a mazabar Ikot Ekpene a yankin Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a jihar.
Leadership ta tattaro cewa iyayen marigayin sun bukaci gawar mamacin da kuma tabbatar da yin bincike don musu adalci.
Sakataren yada labaran jam’iyyar APC, Barista Udo OtoAbasi ya tabbatar da faruwar lamarin.
Martanin iyayen marigayin
Udo ya ce matasan sun yi wa Ime dukan rashin tausayi inda ya ce har yanzu ba a samu labarin inda gawar tashi ta ke ba bayan kwanaki tara.
Har ila yau, iyayen sun tabbatar da cewa bayan masa tsinannen duka an dauki gawar a cikin mota zuwa wani wuri da ba a sani ba, cewar Newswire.
Mahaifin marigayin ya ce:
“Ina bukatar ganin yaro na ko a mace ko a raye saboda in samu damar binne shi da kaina.”
Akalla mutane 30 sun mutu a Plateau
Kun ji cewa an samu asarar rayuka da dama yayin fadan ‘yan bindiga da sojoji a jihar Plateau.
Lamarin ya faru ne da safiyar jiya Asabar 27 ga watan Janairu a kauyuka biyu na karamar hukumar Mangu da ke jihar.
Wannan na zuwa bayan gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita a karamar hukumar bayan barkewar rikici.
Asali: Legit.ng