Tashin Hankali Yayin da Aka Bindige Babban Jigo a PDP, Gwamna Ya Dauki Mataki

Tashin Hankali Yayin da Aka Bindige Babban Jigo a PDP, Gwamna Ya Dauki Mataki

  • Wani mummunan lamari ya faru a Ejigbo da ke jihar Osun, yayin da wani mai gadi ya harbe wani jigon jam’iyyar PDP, Richard Idowu bisa kuskure
  • Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, bayan kammala wani taro wanda Adeoriokin, da abokansa na siyasa, da sauransu suka halarta
  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adekele, ya mayar da martani game da kisan, sannan ya ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ejigbo, jihar Osun - An harbe Farfesa Richard Idowu, wanda aka fi sani da Adeoriokin, wani jigo a jam’iyyar PDP a yankin Ejigbo na jihar Osun.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, lamarin ya ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Asabar, 27 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

An kama 1 daga kasurguman 'yan bindigan da suka sace Nabeeha da 'yan uwanta a Abuja

Adeleke ya ba da sabon umarni
Gwamna Adeleke ya umarci gudanar da bincike kan kisan jigon PDP Hoto: @DukeofOsun
Asali: Twitter

Lamarin dai ya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin. Richard Idowu ya mutu a cikin yanayi mai cike da cece-kuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa wani mafarauci na yankin ya yi kuskuren yin wannan mummunan harbin.

Bayan faruwar lamarin, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa.

Yadda lamarin ya auku

Lamarin ya faru ne a kan titin Inisha da ke Ejigbo, bayan kammala taron da Farfesa Adeoriokin ya halarta, abokan siyasarsa, da Yarima Eniola, ɗan Ogiyan na Ejigbo, Oyeyode Oyesosin.

Bayan taron da aka yi a gidan sarkin, an ruwaito Yarima Eniola ya umarci jami’in tsaron da ya yi harbi cikin iska domin yi wa abokansa bankwana.

An ce ɗaya daga cikin harbe-harben ya samu ƙafar Farfesan ne har ta kai ga mutuwarsa saboda ya yi asarar jini sosai, in ji jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi musayar wuta da wadanda suka sace shugaban PDP, an rasa rai

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, an ajiye gawar Farfesan a ɗakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na jami’ar jihar Osun.

Mutuwar Adeoriokin: Gwamnan Osun ya mayar da martani

Bayan faruwar lamarin, gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Olawale Rasheed, ya fitar a safiyar Lahadi, 28 ga watan Janairu, ta tabbatar da hakan.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Abin da ya faru a Ejigbo abin baƙin ciki ne matuƙa. Ina miƙa ta'aziyyata ga iyalan mamacin. Na ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan kisan da aka yi wa Dakta Richard Adeoriokin da kuma kashe wanda ya kashe shi.
"Na kuma umarci rundunar ƴan sandan jihar da ta fitar da ƙa’idojin amfani da bindigogin gida.

Ƴan Bindiga Sun Nemi Kuɗin Fansa Kan Shugaban PDP da Suka Sace

Kara karanta wannan

An rantsar da Ododo matsayin sabon gwamnan jihar Kogi, wa'adin Yahaya Bello ya kare

A wani labarin kuma, kun ji cewa Miyagun da suka yi garkuwa da shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas, Philip Aivoji, sun aiko da saƙon buƙatar a biya kuɗin fansa.

Masu garkuwan sun buƙaci a tattaro musu Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa kafin sako babban ɗan siyasan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel