Ana Daf da Auren Malamin Makarantar Allo, Matsafa Sun Yanke Mazakutarsa a Zaria
- Rahoton da muke samu ya bayyana yadda wasu matsafa suka yanke al’aurar wani malamin makarantar allo a Kaduna
- An yiwa malamin kisan gilla kafin daga bisani aka gano tuni an yanke wani sashe na jikinsa, lamarin da ya tada hankali
- Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace a halin yanzu ana ci gaba da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Soba, jihar Kaduna - Wani rahoto mai daukar hankali ya bayyana yadda wasu matsafa suka yanke mazakutar wani malamin allo a unguwar Awai da ke karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.
An ruwaito cewa, matsafan sun yiwa mutumin mai suna Alaramma Salisu Mai Almajirai yankan rago tare da yi masa aika-aikar yanke mazakutarsa a hanyarsa ta dawowa daga karbo kayan cin angoncinsa.
Rufa’i Waziri, Sarkin Awai ya shaidawa Aminya cewa, mazauna yankin sun shiga tashon hankali a sadda suka tsinci gawar Alaramma a yashe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka gano an yi masa barna a jikinsa
Ya kuma bayyana cewa, sun gano an cire mazakutarsa ne bayan da aka gano gawar kwance a wani wuri a yankin.
Hakazalika, ya ce wannan bawan Allah da aka kashe mutumin kirki ne, kuma ba shi da abokin fada ko hatsaniya a Awai.
Sarkin ya yi addu’ar Allah ya tona asirin wadanda suka yi wannan bakin aiki, inda ya nemi hukumomin tsaro da su yi aikin gano wadanda suka yi kisan gillar.
Matar marigayi ta magantu
Uwar gidansa, Malama Zulaihat ta shaidawa jaridar yadda lamarin ya faru, inda ta ba da labarin har yadda ta tuntubi budurwar da zai aura don sanin inda yake.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandar Jihar Kaduna ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace a halin yanzu ana ci gaba da bincike don gano mashekan.
Ana yawan samun rahotannin kisan gilla a bangarori daban-daban na Arewacin Najeriya, hakan ba zai rasa nasaba da rashin tsaro da ke addabar yankin ba.
An kama dan bindiga a Kaduna
A wani labarin, rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar 20 ga watan Janairun 2024 sun kame Muhammad Bello, wani matashi mai shekaru 28 dan asalin Zamfara a jihar Kaduna.
Ana zargin Bello na daya daga masu garkuwa da mutanen da suka addabi al’umma da sace-sace a yankin.
Babban jami’in ofishin yanki na Tafa ya bayyana cewa, an kai ga kame matashin ne bayan samun bayanan sirri, inda aka yi ram dashi a wani otal da ke yankin Tafa a Kaduna.
Asali: Legit.ng