CBN, FAAN: Manyan Dalilai 3 da Dattawan Arewa Ke Yakar Tinubu a Kai

CBN, FAAN: Manyan Dalilai 3 da Dattawan Arewa Ke Yakar Tinubu a Kai

  • Matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na dauke wasu sashi na babban bankin CBN da FAAN daga Abuja zuwa Legas ya fusata masu ruwa da tsaki a arewa
  • Duk da cewa gwamnati ta adi hujjarta, dattawa da ‘yan siyasar arewa sun nuna adawa, tare da nuna damuwarsu kan cewa a nan gaba za a kwashe wasu hedkwatarsu daga Abuja
  • Arewa na kara adawa da hakan ne saboda fargabar durkushewar Abuja, da zargin “cabal” din Legas a gwamnatin Tinubu, da kuma tsaron rasa ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - A kwanan nan ne gwamnatin tarayya ta yanke shawarar dauke wasu manyan ofisoshin CBN da hukumar FAAN daga Abuja zuwa Legas.

Koda dai gwamnatin Najeriya ta yi bayanin cewa an dauki matakin ne duba da yanayin aiki, wasu dattawa da yan siyasar arewa sun yi adawa da hakan sosai.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Ƴan bindigan da suka sace shugaban PDP na jiha sun aiko da saƙo mai ɗaga hankali

Yan arewa na adawa da mayar da manyan ofisoshi Abuja
Mayar da Manyan Ofisoshi Legas: Manyan Dalalai 3 da Suka Sa Dattawan Arewa Yakar Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sun yi barazanar cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai gamu da illar da ke cikin yin hakan a ta fuskar siyasa a babban zaben 2027.

Dalilin da yasa arewa ke adawa da yunkurin Tinubu

Da take nuni ga wasu majiyoyi, jaridar Nigerian Truibune, a wani rahoto da ta fitar a ranar Lahadi, 28 ga watan Janairu, ta lissafo manyan dalilai uku da suka sa yan siyasar arewa ke adawa da mayar da wasu ofisoshi Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daya daga cikin dalilan da suka bayyana sgine tsoron cewa gwamnatin Tinubu na iya fitar da karin hedkwata daga Abuja idan har ba a yi wa tufkar hanci ba.

A cewar daya daga cikin majiyoyin da aka sakaya sunanta, arewa na zargin cewa gwamnatin Tinubu na yin gwaji ne da CBN da FAAN kuma cewa da zaran an cimma wannan, da yiwuwar a fitar da karin sassa da hukumomi.

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da babban birnin tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani

Zargin kokarin dakushe Abuja a matsayin babban birnin tarayya

Wani dalili da ake zargi kuma shine cewa yan siyasar arewa suna ganin cewa akwai wasu masu mulki daga Legas wadanda ake yi wa lakabi da 'cabal' a gwamnatin Tinubu wadanda basa farin ciki da mayar da Babban birnin tarayya a Abuja.

Suna tsoron cewa Shugaba Tinubu zai dakushe Abuja kafin karshen wa'adin mulkinsa.

Fargabar rasa ayyukan yi a CBN da FAAN

Dalili na uku da majiyoyin suka bayyana shine yunkurin kare wasu manyan mukamai a CBN da FAAN.

A cewar majiyoyin, wasu yan siyasar arewa da ke adawa da matakin da gwamnati ta dauka suna da "mutane da suka dasa a CBN a sirrince" wadanda abun ya shafe su sosai.

Daya daga cikin majiyoyun ta ce yan siyasar sun bi ta kofar baya wajen samarwa mutanensu aiki a manyan sashi na CBN.

Sai dai kuma, mutanen basa bayar da kowani gudunmawa ko kawo ci gaba ga babban bankin kasancewar "ana ganin yawancinsu suna kewayawa unguwannin Abuja har a lokacin aiki", inji majiyar.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji ta tona asirin mutum 2 da ƙarin wasu abubuwa da suka jawo kashe-kashe a Filato

Majiyar ta ci gaba da cewar yawancin ma'aikatan da wannan ya shafa sun gabatar da satifket daga jami'o'in da ke da ayar tambaya a kasashe masu makwabtaka a Yammacin Afrika.

Saboda haka, ana iya harbo jirginsu idan aka koma Legas.

Bugu da kari, wata majiya ta ce an tura kananan ma'aikata da dama a aiki a hukumar FAAN bayan tsohon minista Hadi Sirika ya mayar da hukumar Abuja.

Ana zargin an yi nadin ne bisa ka’idojin gwamnatin tarayya da ke bai wa hukumomi damar daukar ma’aikata daga mataki na daya zuwa shida a ma’aikatan gwamnati daga yankin da hukumar ke aiki.

Sai dai kuma, ana zargin dattawan arewa na tsoron wadannan ma'aikata na iya rasa madafa idan aka mayar da FAAN Legas.

Reno ya magantu kan mayar da manyan ofisoshi Legas

A wani labarin, mun ji cewa Reno Omokri, jigon jam'iyyar PDP ya bayyana mayar da manyan ofisoshin CBN da hukumar FAAN Legas da gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ta yi ba zai illata arewa ta fuskar siyasa ko tattalin arziki ba.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, Omokri ya cemayar da sassan CBN da hedikwatar FAAN zuwa Legas "don ci gaban tattalin arzikin Najeriya ne".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng