An Kama 1 Daga Kasurguman ’Yan Bindigan Da Suka Sace Nabeeha Da ’Yan Uwanta a Abuja

An Kama 1 Daga Kasurguman ’Yan Bindigan Da Suka Sace Nabeeha Da ’Yan Uwanta a Abuja

  • ‘Yan sanda a jihar Kaduna sun yi ram da wani kasurgumin dan bindigan da ya addabi jama’ar Arewa maso Yamma
  • An gano Bello na daga cikin wadanda kai hari Abuja tare da kashe wata dalibar ABU mai suna Nabeeha
  • Ana ci gaba da bincike kafin gurfanar da wannan bawan Allah da aka kama mai barna a doron kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Tafa, jihar Kaduna - Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar 20 ga watan Janairun 2024 sun kame Muhammad Bello, wani matashi mai shekaru 28 dan asalin Zamfara a jihar Kaduna.

Ana zargin Bello na daya daga masu garkuwa da mutanen da suka addabi al’umma da sace-sace a yankin.

Kara karanta wannan

Ana daf da auren malamin makarantar allo, matsafa sun yanke mazakutarsa a Zaria

An kama dan bindigan da ya sace su Nabeeha
An kame kasurgumin dan bindiga | Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda aka kama Bello a Tafa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban jami’in ofishin yanki na Tafa ya bayyana cewa, an kai ga kame matashin ne bayan samun bayanan sirri, inda aka yi ram dashi a wani otal da ke yankin Tafa a Kaduna.

A cewarsa, an kame matashin da tsabar kudi Naira miliyan 2.25, kudin da ake zargin bangare ne na fansan da ya karba, kamar yadda rundunar 'yan sandan ta sanar a shafinta na X.

A lokacin da aka titsiye shi, matashin ya amsa cewa, yana tare da gungun ‘yan ta’addan da suka sace wani Barista Ariyo a Bwari a Abuja a ranar 2 ga watan Janairu.

Hakazalika, ya amsa yana da hannu a kasan da aka yiwa ‘yan matan da aka sace tare da kashe Nabeeha a cikinsu a ranar 13 ga watan Janairun 2024.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani mai yin sojan gona a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar arewa

An ba DPO cin hanci ya ki karba

A yanayi na tsoro da kuma neman ya kubuta, dan bindigan ya yi kokarin ba DPO cin hancin Naira miliyan 1, inda jami’in ya ki karbar cin hancin don martaba aikinsa.

Sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya umarci a tafi da wanda ake zargin ga sashen bincike DFI-IRT.

daga nan IGP ya yabawa DPO na Tafa, SP Idris Ibrahim bisa kokari da kuma martaba aikinsa fiye da abin da zai samu na cin hanci.

Peter Obi ya yi martani kan kisan Nabeeha

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yiwa Nabeeha Al-Kadriyar, daya daga cikin ‘yan uwa matan da aka sace a Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, inda ta kara da cewa satar ta nuna rashin tsaro a Najeriya da kuma rashin kula da halin ‘yan kasarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.