Yan Bindiga Sun Sace Sufetocin Yan Sanda 3 Tare da Bindigunsu
- Wasu yan bindiga da ake zaton makiyaya ne sun yi awon gaba da wasu jami'an yan sanda uku da ke bakin aiki a jihar Delta
- Jami'an tsaron sun bi sahun wani mutum da aka yi wa fashi a garin Ohoror da ke karamar hukumar Ughelli ta arewa, amma sai ba a kara jin doriyarsu ba
- Haka kuma miyagun sun tsere da bindigogin AK47 da harsasai na jami'an yan sandan da ke aikin sintiri a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Delta - Wasu yan bindiga da ake zaton makiyaya ne sun yi garkuwa da jami'an yan sanda uku da ke aiki a PMF 51, Oghara, a garin Ohoror da ke karamar hukumar Ughelli ta arewa, jihar Delta.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, masu garkuwa da mutanen sun kuma yi awon gaba da bindigogin AK47 da harsasan yan sandan, sannan suka tisa keyarsu cikin daji.
An tattaro cewa jami'an tsaron da aka sace suna cikin tawagar yan sanda shida da aka tura hanyar Ughelli zuwa Patani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma bayyana cewa, labarin sace jami'an yan sandan ya haifar da tashin hankali a garin.
Yadda aka sace jami'an yan sanda a jihar Delta
Wata majiya ta yan sanda ta ce an yi awon gaba da jami'an tsaron ne yayin da suke hanyar amsa wani kira mai cike da damuwa, rahoton The Discoverer.
Majiyar ta ce:
“Lokacin da suke kan hanyar, wani matashi mai suna Moses Progress, mai shekaru 22, dan garin Uwheru ya zo ya sanar da tawagar cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun yi masa fashi.
"Sun sace masa wayarsa kirar OPPO da kudi a karkashin wata gada da ke kusa da inda suke yayin da yake tsafe-tsafensa a kogi.
“Saboda haka, shugaban tawagar sintirin ya umurci jami'an yan sandan uku da suka bi mai korafin zuwa wurin da abun ya faru, dauke da bindigogin AK-47.
"Yayin da suke jiran dawowar yan sandan uku, daga bisani sai tawagar ta ga mai korafin kan wani babur da gudu ba tare da jami'anmu ba."
Majiyar ta ci gaba da cewa:
"Da aka tsayar da shi don tambayarsa game da jami'an yan sandan da suka bi shi. A nan ne ya fada masu cewa, da suka isa wajen, makiyayan su shida sun farmake su a jejin sannan sun tsere yayin da jami'an tsaron suka yi wurare daban-daban.
"Da ya fada ma jami'anmu cewa bai san inda jami'an yan sandan da suka bi sahunsa suke ba, babu wani zabi da ya wuce kama shi sannan suka yi kira a tura masu bin sahu."
Ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, Bright Edafe, ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Yan bindiga sun halaka yan sanda
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu ƴan bindiga da suka yi sanya kayan mata, sun kai hari a wani shingen bincike na ƴan sanda da ke kan hanyar Jibia zuwa Batsari a Katsina.
Jaridar Daily Trust ta ce ƴan bindigan a yayin harin sun kashe sufeto biyu a ƙauyen Gurbin Magarya.
Asali: Legit.ng