An Kawo Jami’ai 140 Su Auna Ministoci, Su Bada Shawarar Wadanda Za a Bari a Ofis

An Kawo Jami’ai 140 Su Auna Ministoci, Su Bada Shawarar Wadanda Za a Bari a Ofis

  • Akwai ma’aikata 140 da aka nada domin su rika lura da ayyukan ma’aikatun gwamnatin tarayya
  • Hadiza Bala-Usman take jagorantar auna kokarin ministocin da Bola Ahmed Tinubu ya nada a ofis
  • Ra’ayin masana ya sha bam-bam a game da wannan sabon tsari da aka kawo a gwamnati mai-ci

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Jami’ai akalla 140 za suyi aikin aunawa da bibiyar kokarin ministoci da shugabannin ma’aikatu na gwamnatin tarayya.

Wani rahoto da Tribune tayi tarayya wajen kawo shi ya nuna zuwa karshen watan nan za a fara bibiyar aikin jami’an gwamnatin kasar.

Ministoci
Ministoci a taron FEC Hoto; State house
Asali: Twitter

Jami'ai masu lura da Ministoci

Wadannan jami’ai da aka dauko sun halarci taron bita na musamman da aka shirya masu.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: Kwanaki 3 da Suka Wuce Tinubu Ya Saki Kudin Manyan Ayyuka 3 Inji Minista

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani babban ma’aikaci da ke kusa da Hadiza Bala-Usman yace wadanda aka dauko za su duba abin da ake yi a ma’aikatu da hukumomi.

Aikin zai shafi shugabannin ma’aikatu, hukumomi da kuma cibiyoyi 35 a Najeriya a karkashin jagorancin tsohuwar shugabar ta NPA.

Yadda za a binciki Ministoci

Daga cikin wadanda za a auna katabus dinsu akwai darektocin tsare-tsare, manyan sakatarori da jami’ai hudu daga duk ma’aikatun.

Majiyar ta fadawa Punch shugaban kasa watau Bola Ahmed Tinubu zai sallami duk wani wanda bai tabuka abin kirki kan kujerarsa ba.

Jami’an da aka ba nauyin auna masu mukaman su ne kashin bayan gwamnati mai-ci.

Akwai ma’aunan da za ayi amfani da su domin gane ministan ko sakataren ma’aikatar tarayya da yake abin a yaba ko akasin haka.

A rabu da Ministoci ko kuwa?

Kara karanta wannan

Da gaske ake yi: Hadimar shugaban kasa ta fadi rukunin Ministocin da za a sallama a ofis

Mike Ozekhome wanda babban lauya ne yana da ra’ayin cewa bibiyar ministocin bai kamata ya zama abin da za maida hankali a kai ba.

Lauyan yace an yi wa kasar kaca-kaca, kuma ana fama da kuncin talauci da rabuwar kai, don haka zai fi kyau ne ayi kokarin kawo gyara.

Wani lauyan ya nuna zai yi wahala a iya auna minista, a ra’ayinsa zai yi wahala son kai bai shigo ba, bai goyon bayan tsarin da aka kawo.

An taso Ministan tarayya a gaba

Henry Dele Alake yana ganin ta kansa a sanadiyyar fasa-kwan manyan da ke satar ma’adanan kasa kamar yadda aka samu rahoto a baya.

Ministan harkokin ma’adanan yace mala’u suna agazawa wajen kawo matsalar rashin tsaro da ta’adanci, hakan ya kawo masa barazana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng