Bidiyon Yadda Abba Gida-Gida Ya Sauko Daga Motarsa Don Ba Wata Hakuri, Sun bugi Motarta Ne

Bidiyon Yadda Abba Gida-Gida Ya Sauko Daga Motarsa Don Ba Wata Hakuri, Sun bugi Motarta Ne

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sauko daga cikin motarsa inda ya isa gaban wata matashiyar mata don bata hakuri
  • Ayarin motocinsa ne suka buga wa matar motarta yayin da suke kan hanya kuma nan take ya nemi yafiyarta
  • Gwamnan ya bukaci matar da ta yi hakuri yayin da ya tabbatar mata da cewar zai yi maganin abun da kansa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shakka babu daga cikin abubuwan da ke sa shugaba ko jagora ya samu karbuwa da zama abun soyuwa a wajen talakawansa, shine zama mai tawali'u da saukin kai.

Hakan ne ya kasance a bangaren gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda a lokuta da dama ya nuna lallai shi mutum ne da bai dauki duniya da fadi ba.

Kara karanta wannan

Matashi da ya mallaki naira miliyan 30 ya samu karayar arziki, ya koma rokon N2k

Gwamnan Kano ya fito daga motarsa don ba wata mata hakuri
Bidiyon Yadda Abba Gida-Gida Ya Sauko Daga Motarsa Don Ba Wata Hakuri, Sun bugi Motarta Ne Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Ya kara tabbatar da hakan ne a lokacin da gwamnan Kanon ya fito cikin tawagarsa a hanyarsu ta zuwa ko dawowa daga wani waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba Gida-Gida ya sauko daga motarsa don ba wata hakuri

Ayarin motocin gwamnan sun daki motar wata matasiyar mata bisa kuskure a yayin da suke jerowa.

Maimakon su yi wucewarsu a matsayinsu na masu madafun iko, ko kuma a tura wani ya bata hakuri, sai Abba ya yi abun da ba a taba tsammani ba.

Gwamnan da kansa ya sauko har zuwa inda matar, wacce zaune a cikin motarta take, sannan ya kuma bata hakuri da neman afuwarta.

An jiyo Abba Gida-Gida a cikin wani bidiyo da ya yadu yana cewa:

"Kina lafiya? ya gajiya?, Na ga yadda suka yi maki ayi hakuri, zan yi maganinsu, nagode."

Kara karanta wannan

"Ku tuba ko a sheke ku": Wike ya gargadi masu garkuwa da mutane da masu yi masu leken asiri

Matashiyar wacce ke cike da farin cikin wannan karamci na gwamnan ta amsa cikin sakin fuska tare da yi masa godiya sannan ta shiga sahun masu daga hannu don jinjinawa gwamnan.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Damilola1017 ta yi martani:

"Mutumin mutane."

@ibabdullahee ya ce:

"Tasan zaizo tayi sauri ta kafa kamara dinta."

@Pointfview ya ce:

"Direbobin jerin gwano basu da hankali dama ko kadan Wlh. An gode Gwamna Abba."

@ebubec1 ya tambaya:

"Shin ya yi tsare-tsaren biyan barnar da aka yi?"

@MrGhata:

"Wannan ya nuna alamar tawali'u."

@s__kabeer:

"Gaskiya mun yi sa'ar samun Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnanmu."

@MuazIdris8:

"Allah mungode ma.
"Mu kam munyi dacen gwamna gaskiya"

Legit ta nemi jin ra’ayin wasu mata kan wannan abu da Abba ya yi.

Malama Amina Muhammad ta ce:

“Gaskiya gwamnan ya nuna cewa shi din namiji ne mai halin dattako kuma wanda ya san darajar diya mace.

Kara karanta wannan

Kano: Bayan kan-kan da kai da bai wa wata mata hakuri, Abba Kabir ya ja kunnen mukarrabansa

“Da wani ne koda bai kai matsayin da shi yake kai ba zai ga kamar zubar da kai ne ba mace hakuri. Allah ya yi wa mutanen Kano babban tagomashi tunda ya hada su da mutumin da ya san darajar dan adam a matsayin shugaba.”

Malama Fatima Abdullahi kuwa cewa ta yi:

“Ni ba masoyiyar Abba bace a baya amma wannan abu da ya yi yasa ya yi kima da daraja a idanuna.
“Ina matukar son ganin an karmama ‘ya mace, a daraja ta a ko’ina kasancewar Allah da manzonsa ma sun daraja ta.
“Lallai Abba jagora ne nagari kuma mai kankan da ki, domin ba kowani namiji ne zai iya abun da ya yi ba musamman idan ya samu kansa a matsayin da shi yake kai a yanzu.”

Ganduje yana zawarcin gwamnan Kano a APC

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga Alhaji Abba Kabir Yusuf ya shigo jam’iyya mai mulki.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana so magajinsa ya yi watsi da NNPP, Daily Nigerian ta fitar da wannan rahoto a yammacin yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng