Ministan Makamashi Ya Fadawa 'Yan Najeriya Abin Da Ya Janyo Musu Karancin Wutar Lantarki

Ministan Makamashi Ya Fadawa 'Yan Najeriya Abin Da Ya Janyo Musu Karancin Wutar Lantarki

  • Matsalar karancin wutar lantarki batu ne da ya dade yana cinye wa yan Najeriya tuwo a kwarya kuma gwamnatoci ke kokarin magance shi musamman na baya-bayan nan
  • Cif Adebayo Adelabu, Ministan Makamashi ya shaidawa 'yan Najeriya cewa karancin iskar gas ne ya janyo matsalar wutar lantarkin na baya-bayan nan saboda basusuka da kamfanonin ke bi
  • Ministan ya bada tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta fara kokarin ganin yadda za a biya basusukan da kamfanonin samar da gas ke bi domin su cigaba da sakin gas din yadda ake bukata don samun lantarkin

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Ministan Makamashi, Cif Adebayo Adelabu, ya danganta karancin wutar lantarki da ake fama da shi a yanzu da raguwar iskar gas da kamfanonin kasar ke samarwa.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya gargadi Tinubu yayin da aka sace shugaban PDP, ya hango sabuwar matsala

Sakamakon hakan, ya ce, shine ya janyo raguwar karfin lantarki da ake samu a cibiyoyi, hakan ya shafi lantarki da kamfanonin rarraba wuta ke ba al'umma.

Rashin isashen gas ke janyo karancin wutar lantarki, Adelabu
Ministan Makamashi ya ce karancin gas ke janyo matsalar wutar lantarki ga 'yan Najeriya. Hoto: Bayo Adelabu
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Domin kawo gyara a lamarin, Adelabu, cikin sanarwar da hadiminsa, Mr Bolaji Tunji ya fitar, ya ce gwamnatin tarayya za ta biya basusukan da ake binta domin a kara yawan gas din da ake kai wa kamfanonin samar da lantarki.

Akwai alamu a ranar Juma'a cewa za a iya biyan basusukan cikin yan makonni da ke tafe domin a rika samun gas din da zai wadatar, rahoton Nigerian Tribune.

Rashin iskar gas ya janyo karancin wutar lankarki, Adelabu

A cewar Adelabu:

"Cikin yan makonni da suka shude, an samu ragowar wutan lantarki da aka bai wa yan Najeriya.
"Hakan ya faru ne saboda karancin iskar gas da ake bai wa kamfanonin samar da lantarki.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani mai yin sojan gona a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar arewa

"Hakan ya yi sanadin raguwar wutan da ake turawa cibiyoyi, wanda hakan ya shafi lantarkin da kamfanonin rarraba wuta ke iya fitarwa.
"Gwamnatin tarayya na kokarin ganin an biya basusuka da kamfanonin samar da lantarki ke bi don inganta samar da gas da karin makamashi; hakan zai taimakawa kamfanonin rarraba wuta su bai wa yan Najeriya karin wuta."

Yayin da ake kukan karancin wutar lantarki, an samu baraka ta kara yin kasa

A wani rahoton, Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, ya ce karancin wutar lantarkin da ake fama da shi a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon barna a wasu kamfanonin da ke amfani da iskar gas a fadin kasar nan.

Barna a bututun Trans-Forcados a watan Disamba ya shafi manyan tashoshin wutar lantarki da suka hada da Olorunsogo, Omotosho, Sapele, Ihovbor, Geregu da Ugheli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164