Yan Bindiga Sun Kashe Matar Ɗan Sanda da Surukarsa a Wata Jihar Arewa

Yan Bindiga Sun Kashe Matar Ɗan Sanda da Surukarsa a Wata Jihar Arewa

  • Yan bindiga sun kashe matar wani dan sanda tare da surukarsa a jihar Neja bayan neman naira miliyan 30 kudin fansa
  • An ruwaito cewa 'yan bindigar sun sace matar da jaririn ta da kuma mahaifiyarta a ranar Larabar da ta gabata, amma sun maida jaririn
  • An gano gawarwakin matan biyu ne a kauyen Apo da ke karamar hukumar Tafa, inda aka ga harbin bindiga a jikin su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Tafa , Neja - Wasu ‘yan bindiga sun kashe matar wani dan sandan Najeriya tare da surukarsa a jihar Neja. Lamarin ya faru ne a unguwar Zhib dake karamar hukumar Tafa a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan bindigar suka kutsa cikin harabar gidan dan sandan suka yi awon gaba da matar da mahaifiyarta.

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

Yan bindiga sun kashe matar ɗan sanda da surukarsa a jihar Neja
Yan bindiga sun kashe matar ɗan sanda da surukarsa a jihar Neja. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Sun raunata dan sandan har ya suma, kafin su yi awon gaba da matarsa ​​tare da jaririn da ta haifa, da kuma mahaifiyarta, wacce ta zo ne don taimaka mata da bukatunta na haihuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindigar sun kashe matan ta hanyar harbi da bindiga

Kwamandan ‘yan banga na garin Gauraka, Sabo Abdullahi ya tabbatar da kashe matan guda biyu a ranar Asabar a zantawarsa da Daily Trust.

Abo Abdullahi, ya shaida cewa an gano gawarwaki biyu na matan, tare da raunukan harsashi a kusa da kauyen Apo da ke cikin unguwar, nesa kadan da wani sansanin ‘yan fashi.

Ya ce hakan ya faru bayan wadanda suka yi garkuwa da su sun mika jaririn matar ga daya daga cikin wadanda suka sako, inda suka umurce su da su kai yaron unguwar Zhibi.

Abin da ɗan sanda ya ce bayan karbo jaririnsa

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar Kashe Gobara ta ceto wani matashi da bashin miliyan 2 ya sa zai kashe kansa

Wakilin jaridar ya gana da dan sandan, Ogwuche Simon, a gidansa da ke unguwar Zhibi a ranar Alhamis bayan ya bar babban asibitin Maitama, Abuja inda aka ka yi masa magani.

Ya ce ya je unguwar Gauraka a ranar kuma ya dawo da jaririnsa daga ofishin ‘yan sanda da ke unguwar inda aka ajiye shi bayan ya shaida cewa dansa ne.

An tattaro cewa barayin sun bukaci a biya su naira miliyan 30 kudin fansa, kafin daga bisani kuma suka kashe matan biyu.

An ceci wani matashe da ya yi yunkurin rataye kansa a Kano

A wani labarin kuma, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta yi nasarar ceton wani matashi da ya yi kokarin kashe kanshi a kusa da gidan Sarkin Nasarawa.

An ruwaito cewa matashin ya bar takarda dauke da dalilin da ya sa ya yanke shawarar halaka kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.