“A Cuci Maza”: Budurwa Ta Cire Cikon da Ta Yi Wa Mazauninta a Gaban Sahibinta, Ya Girgiza a Bidiyo

“A Cuci Maza”: Budurwa Ta Cire Cikon da Ta Yi Wa Mazauninta a Gaban Sahibinta, Ya Girgiza a Bidiyo

  • Wata matashiyar mata ta tube kaya a gaban sahibinta sannan ta nunawa duniya cewa ita din tana sanya acuci maza a kugunta
  • A lokacin da ta cire kayan jikinta, sai ga acuci mazan da ta sanya a kugunta ya fito baro-baro, nan take kuma ta cire shi ta daura a kafar sahibin nata
  • Matashiyar ta tambayi sauran mata ko mazajensu na sane da cewar suna sanya acuci maza ne don samun sura mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar mata ta cire kayan jikinta a gaban sahibinta duk da cewar ta sanya acuci maza a kugunta.

A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok, an gano matashiyar mai suna Sophy Cindy, tsaye a gaban sahibinta, wanda ke zaune a kan wata kujera.

Kara karanta wannan

Dan yahoo ya soki mahaifansa saboda sabulun tsaki da zai kawo mas kudi ya ki aiki, laifinsu 1 tak

Matashiya ta cire a cuci maza a gaban sahibinta
“Acuci Maza”: Budurwa Ta Cire Cikon da Ta Yi Wa Mazauninta a Gaban Sahibinta, Ya Kadu a Bidiyo Hoto: TikTok/@sophy_cindy.
Asali: TikTok

Matashiyar matar ta zuge wandonta kasa sannan ta fara cire kayanta. Da ta sauke dogon wandonta, sai ga acuci maza ya bayyana a kugunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sophy bata tsaya a nan ba, ta cire acuci mazan, kuma yanayin kallon da masoyin nata ya yi ya ba mutane dariya a soshiyal midiya.

Mutumin ya yi martani ta hanyar daura hannayensa biyu a ka tare da bude baki, yana mai nuna mamaki yayin da Sophy ta jefa masa kugun acuci maza da ta sanya.

Bidiyon ya haddasa cece-kuce yayin da Sophy ta tambayi sauran mata ko mazajensu na sane da cewar suna sanya acuci maza a kugunsu.

Ta rubuta:

"Shin sahibinki ya san kina saka acuci maza na mazauni?"

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Opeyemi Ogunsanwo Ch ta ce:

Kara karanta wannan

"Matata ta mayar da hankali kan harkokin addini bata kula da ni", miji ya nemi a raba aurensu

"Kullun a gabansa nake cire shi; sai ka ji yana yi mun kirari ma washegari; matata jakadiyar acuci maza na kugu."

@babie blackton ta ce:

"Kina da tabbacin ba zai samo wacce ke da na ainahi ba? Yi hakuri idan ba bata maki."

@user7793076959750:

"A ina kika siya don Allah."

@user2816025576849:

"Zan siya nawa ne."

@Hammy Candy ta ce:

"Dole sai kin fada ma kowa sirrinmu?"

Sabon hoton Hadiza Gabon ya tada kura

A wani labarin, mun ji cewa fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon Aliyu Gabon, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta saki wani sabon hotonta.

A baya dai jarumar ta kasance irin dirarrun matan nan wadanda ake kira da yan duma-duma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng