Acuci maza: Hoton tsohuwa mai shekaru 75 ta koma tsuleliyar budurwa ya janyo cece-kuce

Acuci maza: Hoton tsohuwa mai shekaru 75 ta koma tsuleliyar budurwa ya janyo cece-kuce

  • Masu kwalliya a zamanin nan na cigaba da baiwa jama'a mamaki ta yadda suke iya mayar da tsohuwa yarinya a take
  • Mahaifiyar Priscilla Appiah ta cika shekaru 75 kuma diyarta ta rangada mata kwalliyar da tasa ta koma tamkar mai shekaru 16
  • Sakamakon da aka samu na wannan kwalliyar kuwa ya baiwa jama'a mamaki inda suka dinga tunanin ba mutum daya bace

Wata mai kwalliya mai suna Priscilla Appiah ta samu jinjina da yabo daga masu amfani da kafar sada zumunta.

Kwalliya ta rangadawa mahaifiyarta wacce ta mayar da tsohuwar mai shekaru 75 zuwa tsuleliyar budurwa mai shekaru 16 kuma ta hada hotunan ta wallafa a Instagram.

KU KARANTA: Katuwar Giwa ta Fada Gidan Wata Mata Neman Abinci, Jama'a Sun Dinga Mamaki

Acuci maza: Hoton tsohuwa mai shekaru 75 ta koma tsuleliyar budurwa ya janyo cece-kuce
Acuci maza: Hoton tsohuwa mai shekaru 75 ta koma tsuleliyar budurwa ya janyo cece-kuce. Hoto daga HB Elegance
Asali: Instagram

KU KARANTA: Borno: Kwaleji ta dakatar da daliba saboda bata fita tarbar Buhari ba

A yayin wallafa hotunan, @hb__elegance ta rubuta: "Barka da cikar ki shekaru 75 mama. Ki girma da karko."

Hoton asalin fuskar mutum da ta kwalliya

A cikin kwanakin nan, masu kwalliya a Najeriya na cigaba da bayyana kwarewasu kuma hakan yana nuna karfin abinda kwalliya za ta iya.

Idan ba a saka dukkan hotunan ba, mutane da yawa kan dage kan karyata cewa ba mutum bane aka yi wa kwalliya ya sauya kamanni. Hakan yasa masu kwalliya ke hada hotunan da da kuma na kwalliyar.

Tsawon wanne lokaci aka dauka yayin yin kwalliyar nan?

A yayin magana da Legit.ng, mai kwalliyar ta ce ta kwashe sa'a daya tana gwangwaje fuskar mahaifiyarta.

Priscilla ta ce ta kwashe shekaru bakwai tana yi wa jama'a kwalliya kuma tana matukar gamsuwa idan ta ga jama'a sun ji dadin aikinta.

A kalamanta: "Na kan fada nishadi idan na saka murmushi a fuskokin mata bayan sun ga yadda na mayar da su."

Jama'a sun dinga jinjinawa mai kwalliyar

@creamybrushes cewa tayi: "Inaa, inaa. Babu abinda zan ce... kin iya sosai."

@teefoli tsokaci tayi da: "Hatta iyalanta ba zasu ganeta ba."

@sexyvirgostyle ta ce: "Kin mayar da ita tamkar mai shekaru 25."

A wani labari na daban, a kalla mutum daya aka kashe kuma aka sace 33 bayan harin da wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Channels Tv ta ruwaito, lamarin ya faru ne a daren jiya a cikin garin Kachia kuma hakan ya bar jama'a da dama da raunika.

Hakimin Kachia, Idris Suleiman ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da jami'an tsaro da suka samu jagorancin kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel