An Yi Zanga-Zanga Yayin da Malamin Makaranta Ya Yi Wa Dalibi Duka Har Sai da Ya Bakunci Lahira

An Yi Zanga-Zanga Yayin da Malamin Makaranta Ya Yi Wa Dalibi Duka Har Sai da Ya Bakunci Lahira

  • Al'ummar garin Oko Afo da ke jihar Legas sun shiga tashin hankali yayin da wani abun bakin ciki ya faru a daya daga cikin makarantun yankin
  • An rahoto cewa wani malamin makarantar mai suna Oluwale, ya yi wa daya daga cikin dalibansa, David Babadipo duka har sai da ya bakunci lahira
  • Wannan al'amari ya haddasa tashin hankali, inda dalibai suka gudanar da zanga-zanga kan mutuwar abokin karatunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Ana zaman dar-dar a makarantar sakandare ta Araromi Ilogbo da ke Oko Afo, jihar Legas, bayan mutuwar wani dalibi, David Babadipo, wanda ake zargin dukan da wani malami ya yi masa ne ya yi ajalinsa.

Wasu bidiyoyi da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno dalibai cikin tashin hankali, suna ikirarin cewa wani malami mai suka Oluwale ya yi wa David duka har sai da ya bar duniya a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini ya gargadi Tinubu yayin da aka sace shugaban PDP, ya hango sabuwar matsala

Malamin makaranta ya zane dalibi har lahira
An Yi Zanga-Zanga Yayin da Malamin Makaranta Ya Yi Wa Dalibi Duka Har Sai da Ya Bakunci Lahira Hoto: @hollaoflagos/Jubril Gawat
Asali: Twitter

Lamarin wanda ya afku a ranar Alhamis, ya haddasa zanga-zanga a tsakanin daliban makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da mutuwar dalibi a Legas

Jaridar Leadership ta rahoto cewa an kwashi Babadipo wanda ya shafe kwanaki yana rashin lafiya zuwa asibiti bayan faruwar lamarin, inda a nan ne aka sanar da mutuwarsa.

Bidiyon da ke yawo ya nuna hargitsi a makarantar, inda dalibai suka dungi gudu cikin rudani.

An jiyo wata muryata a bidiyon tana ikirarin cewa Babadipo ya yi yunkurin fita daga harabar makaranta ne don siyan wani abu lokacin da aka yi masa dukan da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Wani mai amfani da Facebook, Bangose Jide, ya bayyana sunan malamin a matsayin Mista Olawale, mataimakin shugaban makarantar.

Sannan ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ofishin yan sanda da ke Morogbo a Badagry, jihar Legas. Marigayi Babadipo ya kasance dan asalin Ipoti a jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji ta tona asirin mutum 2 da ƙarin wasu abubuwa da suka jawo kashe-kashe a Filato

Sai dai kuma, wata mai amfani da Facebook mai suna Esther Wusu, ta yi korafi cewa Oluwale ne mataimakin shugaban makarantar kuma bai zane David ba.

Sun yi ikirarin cewa tun a ranar Talata yake rashin lafiya sannan malamai sun shawarci iyayensa a kan su zo su kai shi asibiti.

Wata mai amfani da soshiyal midiya, Mama Sassy D, ta yi martani kan lamarin, tana mai nuna cewa an fara rikici, sannan ta nuna damuwa kan tsaron malamin.

Zuwa yanzu, kakakin yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, bai tabbatar da ko an kai rahoton lamarin ga rundunar yan sanda ba, rahoton Osun Defender.

Iyaye sun fusata kan dukan dansu

A wani labarin, mun ji a baya cewa rundunar Yansandan jahar Legas ta gurfanar da wani Malamin makaranta dan shekara 33 mai suna Dare Olaleye gaban wata babbar kotun majistri biyo bayan zane wani dalibinsa mara kunya da yayi, har ya ji masa rauni.

Dansanda mai kara, Benson Emuerhi ya bayyana cewa Malam Dare ya aikata wannan laifi ne a ranar 29 ga watan Maris a tsakanin karfe 11 na safe da karfe 1 na rana a makarantar sakandari ta Camp David dake unguwar Ogba jahar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng