Wani Malami ya gamu da fushin iyaye bayan ya zane yaronsu a makaranta

Wani Malami ya gamu da fushin iyaye bayan ya zane yaronsu a makaranta

Rundunar Yansandan jahar Legas ta gurfanar da wani Malamin makaranta dan shekara 33 mai suna Dare Olaleye gaban wata babbar kotun majistri biyo bayan zane wani dalibinsa mara kunya da yayi, har ya ji masa rauni.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dansanda ma kara, Benson Emuerhi ya bayyana cewa Malam Dare ya aikata wannan laifi ne a ranar 29 ga watan Maris a tsakanin karfe 11 na safe da karfe 1 na rana a makarantar sakandari ta Camp David dake unguwar Ogba jahar Legas.

KU KARANTA: Jerin wasu tsofaffin gwamnoni guda 9 da Buhari zai nada mukamin minista

A cewar Dansandan “Malamin yana daya daga cikin lura da dalibai masu zana jarabawa a makarantar, a wannan rana ya umarci daliban aji 4 da 5 su fita daga dakin zana jarabawar, a lokacin da suke fita ne sai dalibin mai suna Daniel Agboola dan aji 4 ya jefi malamin.

“Wannan ne ya harzuka Malam Dare, inda ya sa tsumagiya ya bullae Dare, a sanadiyyar haka ya ji masa rauni a ido, wanda har sai ta kai ga an yi masa tiyata a idon, kuma hakan ya saba ma sashi na 173 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas.” Inji shi.

Sai dai da aka tambayi Malam Dare ko ya amsa tuhumar da ake yi masa, sai Malam Dare ya kada yace “Bai amsa laifinsa ba, kuma bai aikata ba.”

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkalin kotun, Olufunke Sule-Amzat ta bayar da belin Malamin a kan kudi N50,000, tare da mutum daya da zai tsaya masa shima a kan kudi N50,000.

Daga nan ta bayar da umarnin a garkame Malamin a kurkuku zuwa lokacin da zai cika sharuddan beli, sa’annan ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Oktoban 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel