Garba Shehu Ya Fadi Kuskuren Da ’Yan Najeriya Suka Yi Wa Buhari, Ya Roki Kada a Maimaita Wa Tinubu

Garba Shehu Ya Fadi Kuskuren Da ’Yan Najeriya Suka Yi Wa Buhari, Ya Roki Kada a Maimaita Wa Tinubu

  • Garba Shehu, hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana kuskuren da aka yi lokacin Buhari
  • Garba ya ce babban kuskuren da ‘yan Najeriya suka yi shi ne daurawa Buhari buri kan sauyawar komai lokaci daya
  • Ya ce hakan kuskure ne kuma bai kamata a sake yin wannan kuskure a gwamnatin Bola Tinubu ba a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya shawarci ‘yan Najeriya kan kuskuren da su ka yi a baya.

Garba ya ce babban kuskuren da ‘yan Najeriya suka yi shi ne daurawa Buhari buri kan sauyawar komai lokaci daya, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da babban birnin tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani

Hadimin Buhari ya gargadi 'yan Najeriya kan kuskurensu a baya
Garba Shehu ya ce an tafka kuskure a lokacin Buhari. Hoto: Bola Tinubu, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Mene Garba Shehu ke cewa kan Buhari?

Ya roki ‘yan Najeriya da kada su maimaita kuskuren ga gwamnatin Shugaba Tinubu kan tsammanin samun komai a gwamnatin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu ya yi wannan rokon ne a yau Juma’a 26 ga watan Janairu yayin taron karawa juna sani da Daily Trust ta dauki nauyi.

Tsohon hadimin ya ce burin da aka daurawa gwamnatin Buhari ita ne babbar matsalar da ya samu.

Shawarar da ya bai wa 'yan Najeriya

Ya shawarci ‘yan Najeriya da su rage wannan buri ga gwamnatin Tinubu don samun abin da ake nema.

Har ila yau, ya bukace su da su koyi darasi kan abin da ya faru a gwamnatin baya don kada su daura rai kan abin da ba zai samu ba.

Ya ce:

“Buhari ya shiga matsala ne kan yawan buri da ‘yan Najeriya suka daura masa, wannan darasi ne da ya kamata mu koya.

Kara karanta wannan

"Kada ku mayar da kudi Ubangijinku": Tinubu ya ba shugabannin Kirista babban aiki 1 tak

“Saboda wannan yawan buri da tsammani bai kamaci dan Adam ba, shugabanni za su yi abu da yawa amma ba komai ba.”

Adesina ya fadi dalilin barin zuwa coci

Kun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya bayyana irin rayuwar da ya yi lokacin da ya ke Abuja.

Adesina ya ce musamman ya bar zuwa coci saboda Faston ya na yawan caccakar gwamnatin Buhari.

Hadimin ya bayyana haka ne a wani littafiin da ya wallafa ‘Working with Buhari’ da ke dauke da abubuwa game da rayuwarsa da Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.