Hadimin Buhari Ya Fadi Yadda Ya Bar Zuwa Wurin Ibada Kan Zagin Mulkin Baba da Malamin Addini Ya Yi

Hadimin Buhari Ya Fadi Yadda Ya Bar Zuwa Wurin Ibada Kan Zagin Mulkin Baba da Malamin Addini Ya Yi

  • Femi Adesina, hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ya bar zuwa coci kan Buhari
  • Adesina ya ce ya bar zuwa cocin ne saboda yadda Faston ke caccakar Buhari a kullum yayin hudubarsa
  • Femi ya bayyana haka ne a cikin littafin da ya wallafa ‘Working with Buhari’ wanda ke dauke abubuwa daga 2015 zuwa 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hadimin Buhari, Femi Adesina ya bayyana yadda ya bar zuwa coci saboda Fasto ya soki mulkin Buhari.

Adesina ya ce tuni ya dauke kafa a cocin Foursquare da ke Abuja saboda sukar Buhari da Fasto Babajide Olowodola ya yi.

Kara karanta wannan

Kakakin Buhari: Abin da ya hada ni fada da Abba Kyari a Aso Villa har ya rasu

Yadda Adesina ya bar zuwa bautar Allah saboda an zagi Buhari
Femi Adesina Ya Ce Dole Ya Bar Zuwa Coci Kan Zagin Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari, Femi Adesina.
Asali: Facebook

Mene Adesina ke cewa kan Buhari?

Femi ya bayyana haka ne a cikin littafin da ya wallafa ‘Working with Buhari’ wanda ke dauke abubuwa daga 2015 zuwa 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dole ya bar zuwa cocin da ke fadar shugaban kasar a watan Faburairun 2018 saboda son rai na malamin addinin, cewar Tribune.

Ya kara da cewa Faston ya dauka cewa zai iya kifar da Buhari daga irin kalamansa da ya ke fada wa jama’ar cocin.

Wane mataki Adesina ya dauka?

Ya ce:

“Ni mamban cocin Foursquare ne a Najeriya, na dade ina zuwa cocin tun bayan komawa Kiristanci a shekarar 1988.
“A shekarar 2015 da na fara aiki a Abuja na ci gaba da halartar cocin da ke Asorock wanda Fasto Babajide Olowodola ke jagoranta.
“Bayan wasu makwanni sai naji ya fara kalamai inda ya bukaci mambobinsa su tanadi katunan zabensu saboda zaben 2019 don yakar Buhari.”

Kara karanta wannan

Talaka ya tsokano wuyan da ake ciki, mun gargade shi kafin zabe – Tsohon Jigon APC

Adesina ya kara da cewa a 2018 bayan an sace dalibai Dapchi, babu irin munanan kalmomi da Faston bai kira Buhari da su ba, cewar Newstral.

Bayan an samu kubutar da daliban, Femi ya ce ya je ko Fasto zai yabi Buhari amma ya ci gaba da sukar Buhari, daga nan ya dauki littafinsa ya fice.

Adesina ya bayyana yadda suka yi da Kyari

A wani labarin, Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya fadi yadda suka kai ruwa rana da marigayi Abba Kyari.

Adesina ya ce Kyari mutum mai mugun biyayya ga Buhari amma sun yi ta samun matsala kafin rasuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel