Wike Ya Fusata da Sakacin Ciyamomin Abuja a Matsalar Tsaro, Ya Musu Barazana Kan Abu 1
- Ministan FCT, Nyesom Wike ya gargadi shugabannin kananan hukumomin Abuja kan gaza halartar taron tsaro na wata wata da ake yi
- Wike ya yi wa ciyamomin barazana da cewa duk wanda ya sake ƙin halartar taron zai shiga jerin 'masu barazana ga tsaron Abuja'
- Ministan ya ce majalisar kananan hukumomin Abuja (AMAC) za ta tallafawa jami'an tsaro wajen yaki da 'yan bindiga
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya caccaki shugabannin kananan hukumomin birnin da suka yi watsi da taron tsaro na wata-wata.
Wike, wanda ya yi magana a wani taro da aka yi a majalisar karamar hukumar Abuja (AMAC), ya ce daga yanzu duk shugaban karamar hukumar da ya gaza halartar taron, za a ayyana shi a matsayin 'barazana ga tsaro'.
Wike ya yi wa iyamomin Abuja barazana
Ministan ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Yaya za ku ce ba ku gudanar da taron tsaro na wata-wata saboda ba ku da alawus? Daga yanzu duk shugaban da ya kasa halartar wannan taro za mu rika kallonsa a matsayin barazana ga tsaro”.
Ya ba da tabbacin cewa hukumar za ta yi duk mai yiwuwa don tallafa wa jami’an tsaro, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tun da farko, shugaban AMAC, Christopher Maikalagiu, ya yaba wa Wike bisa abin da ya kira "ayyukan raya kasa da yake aiwatarwa tun bayan zamansa minista".
Ministan ya umurci shugabannin kananan hukumomin shida na Abuja da su kafa kungiyoyin 'yan sa kai tare da ba shi sunayen mambobin kungiyoyin, a cewar jaridar Leadership.
Yan bindiga sun farmaki 'yan gudun hijira a Taraba
A wani labarin kuma, wasu gungun 'yan bindiga sun bude wuta kan wasu 'yan gudun hijira a kauyen Ikyenum, karamar hukumar Wukari, jihar Taraba.
An ruwaito cewa mutum biyu ne suka mutu nan take yayin da wasu da dama suka samu raunuka a yayin farmakin.
Tun da fari, Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigar da ake zargin 'yan kabilar Jukun ne sun ba 'yan gudun hijirar umurnin ficewa daga muhallansu.
Asali: Legit.ng