Rashawar $500,000: Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci Kan Zaman Farouk a Gidan Yari Na Shekara 5

Rashawar $500,000: Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci Kan Zaman Farouk a Gidan Yari Na Shekara 5

  • Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yi na daure Lawan Farouk shekara biyar gidan gyara hali
  • Lawan, wanda tsohon dan majalisar tarayya ne, ya fara gurfana gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargin karbar cin hanci da rashawa
  • A shekarar 2012 ne aka yi zargin Lawan ya karni cin hancin dala 500,000 daga hannun dan kasuwa Otedola a lokacin badakalar tallafin mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa Farouk Lawan, tsohon dan majalisar wakilan tarayya, zai shafe shekaru biyar a gidan gyaran hali kamar yadda Kotun Daukaka Kara ta ayyana.

A shekarar 2021 ne kotu ta garkame Lawan saboda karbar rashawar dala 500,000 daga hannun dan kasuwa, Femi Otedola, shugaban kamfanin Zenon Petroleum & Gas.

Kara karanta wannan

PDP vs APC: Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari'ar gwamnan jihar Sokoto

Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan zaman Farouk a gidan yari
Rashawar $500,000: Kotun Ƙoli ta yanke hukunci kan zaman Farouk a gidan yari na shekara 5. Hoto: AFT
Asali: Getty Images

Hukuncin daurin shekara biyar

A hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, kwamitin mutane biyar na kotun kolin ya amince da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a shekarar 2022, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru biyar ga Lawan kan tuhume-tuhume uku daga cikin tuhume-tuhumen da aka yi masa a babbar kotun birnin tarayya Abuja.

Mai shari’a John Okoro, wanda ya shirya hukuncin, ya sanar da hukuncin ne ta hannun mai shari’a Tijjani Abubakar. Kotun kolin ta gano karar da Lawan ya shigar ba ta da gamsassun hujjoji kuma ta yi watsi da ita.

Lawan ya karbi cin hancin dalar Amurka 500,000 a 2012

Lawan ya karbi cin hancin dalar Amurka 500,000 a lokacin da yake rike da mukamin shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar da ke binciken badakalar tallafin man fetur a shekarar 2012.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukuncin karshe kan zaben gwamnan APC, komai na iya faruwa

Kotun tarayya ta ce Lawan ya karbi kudin daga hannun Femi Otedola don cire kamfanin Zenon Oil and Gas, daga cikin sunayen kamfanonin da ake tuhuma, Leadership ta ruwaito.

Alkalin kotun, Angela Otaluka, ta ce Lawan na da laifuffuka uku da suka hada da cin hanci da rashawa, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.