Rundunar Soji Ta Tona Asirin Mutum 2 da Ƙarin Wasu Abubuwa da Suka Jawo Kashe-Kashe a Filato
- Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana muhimman abu 2 da suka jawo tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Mangu, jihar Filato
- Kakakin hedkwatar tsaro, Janar Buba, ya ce kisan da wani makiyayi ya yi wa ɗan garin Mangu na cikin abubuwan da suka jawo rikicin
- Ya kara da cewa hedkwatar tsaro zata gayyaci shugaban CAN na karamar hukumar Mangu bisa kalaman da ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana asalin abubuwan da suka haddasa rikicin jihar Filato wanda kawo yanzu ya yi ajalin bayin Allah da dama.
Rundunar ta ce wani makiyayi, satar shanu da wasu abubuwa ne suka haddasa rikicin da ya dabaibaye karamar hukumar Mangu ta jihar Filato a kwanan nan.
Daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja kan ayyukan rundunar sojin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ya ce an tura dakaru na musamman zuwa wuraren da rikicin ya fi ɗaukar zafi a jihar domin shawo kan lamarin, kamar yadda Channels tv ta tattaro.
Menene asalin abubuwan da suka hadddasa tashin hankalin?
A kalamansa, Janar Buba ya ce:
"Asalin tashin hankalin ya faro daga abubuwa da dama, daga cikinsu har da yunƙurin satar shanu da kuma kisan da wani makiyayi ya yi wa mutum ɗaya ɗan garin Mangu."
Ya ce bayanan da aka tattaro sun nuna cewa cewa wani mutumi a kan babur ya ci karo da garken shanu da ke tsallake titin da yake kai ranar 22 ga watan Janairun 2024.
"Nan take masu shanun suka kashe mutumin. Bayan haka kuma wasu tsagerun ciki suka haɗu suka kai farmaki garin washe gari ranar 23 ga watan Janairu."
DHQ zata gana da shugaban CAN na Mangu
Janar Buba ya kara da cewa hedkwatar tsaro za ta gana da shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya na karamar hukumar, Rabaran Timothy Daluk, kan kalaman da ya yi.
Ya ce zasu zauna da shugaban CAN ɗin ne kan zargin da ya yi cewa dakarun soji na da hannu a kashe kiristoci da lalata masu kadarori.
Sama da mutane 30 aka kashe tare da jikkata wasu da dama da kona gidaje lokacin da wasu mahara suka kai hari kauyen Kwahaslalek, ƙaramar hukumar Mangu.
An kama masu hannu a rikicin Filato
A wani rahoton kuma Jami'an ƴan sanda sun kama mutum 17 da ake zargin suna da hannu a kashe-kashen da ke faruwa a jihar Filato.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya nuna dukkan waɗanda aka kama a hedkwatar ƴan sanda a Jos.
Asali: Legit.ng