Emefiele: EFCC Ta Shiga Bibiyar Kamfanonin Kasar Waje a Binciken Dala Biliyan 347
- Babban bankin CBN ya rabawa kamfanoni kudin kasar waje masu yawa a tsakanin shekarun 2014 da 2023
- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC tana zargin wasu kamfanonin ketare suna da hannu a badakalar kudin da aka yi
- Godwin Emefiele wanda aka dakatar daga aiki bayan Bola Tinubu ya rike bankin kasar; CBN a lokacin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gasiya tana binciken yadda aka rabawa kamfanoni $347bn a Najeriya na shekaru kusan goma.
Binciken ya shafi abubuwan da suka faru daga Junairun 2014 zuwa Yunin 2023 kamar yadda Punch ta fitar da rahoto a makon nan.
Abin da hakan yake nufi shi ne hukumar ta EFCC ta fadada binciken rabon kudin kasar wajen da take yi a kamfanonin gida da ketare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A haka aka gano kamfanonin Najeriya da na kasar waje sun samu kusan $350bn daga hannun babban bankin na Najeriya watau CBN.
Alkaluman sna cikin rahoton yadda aka yi amfani da kudin kasashen waje a bankin CBN musamman a lokacin Godwin Emefiele yana ofis.
Tun da Ola Olukoyede ya karbi ragamar hukumar aka fara binciken ayyukan CBN.
EFCC za ta tabo kamfanonin waje
Jaridar tace kamfanonin ketare da za a bincika sun kunshi Crane Currency Limited, Gleseck+Deverint GmbH da kamfanin De La Rue Ltd.
Haka kuma ana binciken abubuwan da suka faru a Oberthur Fiduclaire SAS da Orelll Fussli.
Takardar da aka samu daga EFCC
Wata ma’aikaciyar EFCC, Hadiza Junaidu, ta aika takarda da lamba CB:4000/EFCC/DOPS/VOL.28/104 tana neman bayanan rabon daloli.
Takardar jami’ar ta nuna za a binciki kamfanonin kasashen wajen bisa zargin sabawa dokoki da ka’idojin shiga da fitar da kaya a Najeriya.
Junaidu ta bada umarni a zagaya da takardar zuwa ga sauran jami’an hukumar.
Abin da ba a tabbatar ba shi ne lokacin da bankin CBN zai tsaida bada kudin kasashen waje ga kamfanoni da ke kasuwanci a waje.
EFCC da binciken msu mulki
Akwai tsofaffin gwamnoni daga ciki har da ministocin Bola Tinubu da aka ji suna cikin wadanda EFCC ta ke bincike kan su a halin yanzu.
A jerin akwai tsofaffin gwamnonin Ekiti, Kano, Enugu, Zamfara, Delta, Ribas da Abia.
Asali: Legit.ng