Ana Cikin Jimamin Hare-Haren Plateau, Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Jihar Arewa
- An samu asarar rayukan bayin Allah a wani sabon harin ta'addanci da ƴan bindiga suka kai a jihar Benue
- Miyagun ƴan bindigan sun halaka mutum biyu tare da ƙona gidajen da yawansu ya kai aƙalla guda 17
- Harin na ƴan bindigan ya tilasta mutane barin gidajensu zuwa wasu ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su don samun mafaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Rahotanni sun ce wasu ƴan bindiga sun kashe mutum biyu a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Okpokpolo da ke ƙaramar hukumar Agatu a jihar Benue.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, yankin ya ƙara fuskantar hare-hare a ƴan kwanakin da suka gabata, lamarin da ya sa mazauna ƙauyukan da dama suka bar gidajensu.
Jaridar Daily Post ta tattaro cewa mazauna ƙauyukan dai sun yi ƙaura zuwa wasu ƙauyukan da ke kusa da iyaka da jihar Kogi, musamman bayan kashe jami’an tsaro uku da aka yi kwanan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin sun bayyana cewa, harin na baya-bayan nan wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu, ya faru ne da ƙarfe 10:00 na daren ranar Talata.
Sun bayyana cewa wasu ƙauyuka da dama irin su Ikpele, Ogbai da Okpokpolo, inda aka tsinto gawarwakin, sun fuskanci farmaki wanda ya ɗauki tsawon sa’o’i da dama a daren Talata.
Kazalika mazauna ƙauyen sun bayyana cewa an ƙona gidaje da dama da suka kai aƙalla 17, inda mutanen cikinsu suka gudu suka nemi mafaka a wasu wuraren daban.
Me hukumomi suka ce kan harin?
Mike Inalegwu, tsohon kwamishinan yada labarai a jihar ya tabbatarwa manema labarai a Makurdi cewa ƴan bindigan sun kai hari ƙauyen Okpokpolo tare da kashe mutum biyu, yayin da suka kuma farmaki sauran ƙauyukan.
Sai dai, mai ba da shawara kan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Cif Joseph Har, wanda shi ma ya tabbatar da aukuwar harin, ya ce ba a shaida masa cewa an kashe mutane ba.
Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Benue, SP Catherine Anene, ta bayyana cewa ba ta da masaniya kan lamarin.
Sojoji Sun Ragargaji Ƴan Bindiga a Benue
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun ragargaji wasu miyagun ƴan bindiga a jihar Benue.
Sojojin sun kuma samu nasarar ceto wasu mutum tara da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng