Rundunar Yan Sanda Ta Yi Magana Kan Fashewar Wani Abu a Abuja, Ya Tafka Mummunar Ɓarna

Rundunar Yan Sanda Ta Yi Magana Kan Fashewar Wani Abu a Abuja, Ya Tafka Mummunar Ɓarna

  • Rahotanni daga mazauna Abuja sun nuna cewa wani abu da suke kyautata zaton bam ne ya tashi a Anguwar Maitama
  • Amma rundunar yan sandan ta fito ta fayyace gaskiya, inda ta ce wani abun kwashe shara ne na ƙarfe ya yi bindiga sabida abu 1
  • A wata sanarwa, rundunar ta tabbatar da cewa mutum biyu sun samu rauni sakamakon afkuwar lamarin yau Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta fayyace gaskiya kan rahoton da ake yaɗawa na fashewar wani abu da ake zargin 'Bam' ne a Maitama

A cikin jerin sakonnin ake ta wallafawa a manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba, wasu mazauna birnin sun danganta lamarin da tashin bam.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da sabon rikici ya ɓarke tsakanin magoya bayan APC da NNPP, bayanai sun fito

Yan sanda sun faɗi gaskiya kan abun da ya fashe a Abuja.
Yan Sanda Sun Yi Magana Yayin Wani 'Bam' Ya Tashi a Birnin Tarayya Abuja Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Amma rundunar ƴan sandan FCT a wata sanarwa da jami'ar hulɗa da jama'a ta ƴan sanda, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce lamarin ya faru daga kwandon shara na karfe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asalin abinda ya faru a Maitama - Yan sanda

Mai magana da yawun ƴan sandan ta ce wani abun zuba shara na karfe da ya ɗauki zafin da ya wuce kima ne ya yi bindiga amma ba bam ba kamar yadda ake yaɗawa.

A rahoton Daily Trust, SP Adeh ta ce:

"Rundunar ‘yan sandan Abuja ta yi wa jama’a karin bayani kan fashewar wani abu da ya afku a ranar 24/01/2024 da misalin karfe 11:45, kusa da wani juji a wajen harabar ofishin Bureau of Public Enterprise da ke Maitama.
"An tura tawagar kai ɗaukin gaggawa da masu kwance bam wurin domin tantance abinda ya faru kuma binciken farko ya nuna wani kwandon kwashe shara na ƙarfe ne ya fashe bayan ya ɗau zafin da ya wuce ƙima.

Kara karanta wannan

Ana fargabar rayukan mutane da dama sun salwanta a wani sabon rikici a jihar Arewa

"Hakan ya janyo raunata biyu daga cikin masu kwashe shara, wadanda a halin yanzu ke samun kulawar likitoci a babban asibitin Maitama."

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta bukaci jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da kauracewa amfani da kwandon shara na karfe, The Nation ta tattaro.

Boko Haram sun farmaki sojoji Borno

A wani rahoton na daban Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun mamayi dakarun sojin Najeriya, sun buɗe musu wuta a jihar Borno.

Wata majiya daga cikin sojojin ta ce ƴan ta'addan sun kashe soja ɗaya da wasu jami'an tsaro biyu a harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel