Ana Tsaka da Rikicin Kabilanci, Kotu Ta Yi Hukunci Kan Matsalar da Ta Dabaibaye Majalisar Plateau

Ana Tsaka da Rikicin Kabilanci, Kotu Ta Yi Hukunci Kan Matsalar da Ta Dabaibaye Majalisar Plateau

  • Yayin da ake cikin rikici a jihar Plateau, Babbar Kotun Tarayya da ke Jos ta yi hukunci a rikicin korarrun 'yan Majalisun PDP
  • Kotun ta ki amincewa da bukatar PDP kan dakatar kakakin Majalisar daga kaddamar da sabbin 'yan Majalisun APC 16 a zaman Majalisar
  • Hakan na zuwa ne bayan Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben 'yan Majalisun tare da bai wa APC saboda rashin tsari a jami'yyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Babbar Kotun Tarayya da ke Jos ta ki amincewa da bukatar jami'yyar PDP na dakatar da sabbin 'yan Majalisu 16 na APC.

Jami'yyar PDP ta bukaci kotun ta dakatar da rantsar da sabbin 'yan Majalisun yayin da Majalisar ta koma zama a ranar Talata 23 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Kano: Bayan DSS ta cafke Dan Bilki, kotu ta dauki mataki kan zargin cin zarafin Kwankwaso

Kotu ta dauki mataki kan shari'ar Majalisar jihar Plateau
Kotu ta ki amincewa da bukatar PDP a matsalar Majalisar jihar Plateau. Hoto: Plateau Assembly.
Asali: UGC

Wane mataki kotun ta dauka kan matsalar Majalisar?

Kotun Daukaka Kara ta rusa zaben 'yan Majalisun tare da bai wa APC saboda rashin tsari a jami'yyar, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari'a, V D. Agishi ya ce bai kamata su amince da korafin PDP ba na dakatar 'yan Majalisun saboda yanayin shari'ar.

Kotun ta kuma ki amincewa da bukatar PDP kan tilasta kakakin kin tabbatar da su a Majalisar.

Matakin da kakakin Majalisar ya dauka tun farko

Har ila yau, kotun ta kuma yi fatali bukatar jami'yyar kan hana kakakin Majalisar amincewa da satifiket da hukumar INEC ta ba su.

Tun farko PDP ta bukaci kotun ta dakatar da kakakin Majalisar rantsar da sabbin 'yan Majalisun, cewar PM News.

Kakakin Majalisar, Gabriel Kudangbena a ranar Litinin 22 ga watan Janairu ya ce ba zai tabbatar da 'yan Majalisun APC 16 ba.

Kara karanta wannan

Mambobin Majalisar jihar APC sun tsige kakakin Majalisa kan dalili 1 tak, sun nada sabo

Korarrun 'yan Majalisun PDP sun sha alwashi

Kun ji cewa korarrun 'yan Majalisun PDP da aka kwace kujerunsu sun sha alwashin komawa kujerunsu.

Wannan na zuwa ne bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar mambobin jami'yyar APC a matsayin wadanda suka lashe zabe.

Korarrun 'yan Majalisun sun bayyana cewa ba a yi musu adalci ba ganin yadda aka yanke hukuncin a Kotun Daukaka Kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.