Dara za ta ci gida yayin da shugaban EFCC ke fuskantar dauri a gidan kaso kan dalili 1 tak
- Wata babbar kotun birnin tarayya ta ba sufeto janar na yan sanda, ayode Egbetokun, umurnin kama shugaban EFCC, Ola Olukoyede
- Ana zargin Olukoyede da shugaban sashin kula kayayyakin da hukumar ta kwace, Aliyu Yusuf, da saba wani umurnin kotu
- Tsohon dan takarar gwamnan APC a jihar Abia, Ikechi Emenike, ne ya yi karar hukumar bayan ta ki bin umurnin kotu na siyar masa da wani gidansa da aka mallakawa gwamnati
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Ola Olukoyede, Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), na iya fuskantar dauri a gidan gyara hali.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto a yammacin ranar Laraba, 24 ga watan Janairu, Olukoyede da hukumar da yake jagoranta, ta EFCC, sun ki bin umurnin kotu.
Kotu ta umurci IGP da ya kama shugaban EFCC
Kan zargin rashin biyayya, wata babbar kotun birnin tarayya karkashin jagorancin Mai shari'a Abubakar Musa ya umurci Sufeto Janar na yan sanda, Kayode Egbetokun, da ya kama Olukoyede.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta kuma umurci a kama Aliyu Yusuf, shugaban sashin kula da kadarorin da aka kwace a hukumar mai yaki da cin hanci da rashawar.
Jaridar Legit ta rahoto cewa babban jami'in na hukumar yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar barazanar dauri biyo bayan karar da Ikechi Emenike, tsohon dan takarar gwamnan APC a jihar Abia ya shigar.
Emenike ya tunkari kotu ne kan wani gida da aka mallakawa gwamnatin tarayya bisa zargin rashawa.
Wani rahoton kafafen labarai ya ce Emenike ya nemi siyan gidan wanda ya kai sama da naira miliyan 380, amma EFCC ta ki sannan ta tura jami'anta don su toshe duk hanyoyin shiga gidan.
Daga nan sai Emenike ya tunkari kotun yana neman a ba EFCC umurnin ta ba shi damar siyan gidan. Ya bayyana matakin da EFCC ta dauka a kansa a matsayin rashin adalci da zalunci.
An tattaro cewa kotun ta yanke hukunci wanda mai takarar gwamnan ya yi nasara, inda aka bukaci jami'an EFCC su bar gidan dan siyasar.
Rahotanni sun ce EFCC ta ki bin umurnin, lamarin da ya sa Emenike ya fara shari’a da shugaban hukumar mai ci da kuma shugaban kungiyar kwato kadarorin kan kin bin umurnin kotu.
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamna
A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu.
EFCC za ta gurfanar da Obiano a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin almundahanar kudi har naira biliyan hudu.
Asali: Legit.ng