Ministan Buhari Ya Tona Asirin Abin da Ya Jawo Wa Isa Pantami Bakin Jini a Gwamnatinsu
- Yayin kaddamar da littafin Farfesa Isa Pantami, tsohon Minista Fashola ya bayyana abin da ya jawo wa Pantami bakin jini
- Fashola ya ce babban abin da ya sa mafi yawan mutane a gwamnatin Buhari ke jin haushinsa shi ne bin ka'idoji
- Raji Fashola ya bayyana haka ne a yau Laraba 24 ga watan Janairu yayin kaddamar da littafin Pantami a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Ministan ayyuka, Babatunde Fashola ya bayyana abin da ya jawo wa Farfesa Isa Ali Pantami bakin jini.
Fashola ya ce tsohon Ministan Sadarwar ya na wasu abubuwa da ke bata wa wasu mutane a gwamnatin rai.
Mene Fashola ke cewa kan Pantami?
Ya ce babban dalilin shi ne yadda Pantami ke son yin gaskiya da aiki tukuru don ganin an samu abin da ake so, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Ministan ya bayyana haka ne a yau Laraba 24 ga watan Janairu yayin kaddamar da littafin Pantami a Abuja.
Ya ce:
"Na san Isa Pantami yayin da muaka yi aiki tare a matsayin Ministoci a gwamnatin Buhari daga shekarar 2019 zuwa 2023.
"Yadda ya ke son yin komai bisa ka'ida da bin tsari a bayyane ya ke, yadda ya ke bin diddigin aiki ya na bai wa mutane haushi."
Wane yabo Fashola ya yi ga Pantami?
Ya kara da cewa:
"Amma mun samu ci gaba sosai da akidunsa, shiyasa muke kiransa 'Baban bin ka'ida' wanda ya gyara mana ayyuka sosai."
Taron kaddamar da littafin na Pantami ya samu halartar manyan baki kamar su Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da Inuwa Yahaya na Gombe.
Sauran sun hada da Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da tsohon gwamnan jihar Gombe, Muhammad Danjuma Goje, cewar Within Nigeria.
Pantami ya nuna bacin rai game da rashin tsaro
Kun ji cewa tsohon Ministan Sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Pantami ya nuna bacin ransa game da yadda rashin tsaro ke kazanta.
Pantami ya ce ya fi kowa jin haushin yadda matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.
Asali: Legit.ng